Gwamnan APC Ya Sa a Cafke ‘Dan Takara da Shugaban Jam’iyyarsa a Kan Kashe Mutane

Gwamnan APC Ya Sa a Cafke ‘Dan Takara da Shugaban Jam’iyyarsa a Kan Kashe Mutane

  • David Umahi ya ziyarci Ekoli Edda a karamar hukumar Afikpo bayan kisa da kone-konen da aka yi
  • Gwamnan Ebonyi ya bada umarnin gaggawa cewa a damke shugaban APC da ‘dan takarar jam’iyya mai-ci
  • Ana zargin shugaban APC na jihar Ebonyi, Stanley Okoro Emegha ya na da hannu a abin da ya faru a kauyen

Ebonyi - A ranar Talata, 27 ga watan Disamba 2022, Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi ya bada umarni a kama shugaban APC, Stanley Okoro

Vanguard ta ce ana zargin Mista Stanley Okoro Emegha da hannu a mutuwar mutane da kuma kona gidajen jama’a da aka yi a Ekoli Edda da ke garin Afikpo.

Baya ga haka, Mai girma Gwamnan ya kuma bada umarni ayi gaggawar cafke Eni Uduma Chima mai neman takarar ‘dan majalisar tarayya na yankin Afikpo.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Bayyana Abu 1 Da Yan Kaduna Ba Za Su Taba Manta El-Rufai a Kansa Ba

Gwamnan ya bada wannan umarni ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido bayan harin da aka kai wa mutanen kauyen Ekoli Edda, har aka kashe mutane uku.

Ana zargin Emegha.da Chima da laifi

A rahoton Daily Post, an ji cewa ana zargin wadannan ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki su na da hannu a kan abin da ya faru, don haka za a bincike su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya fitar da jawabi ta bakin Chooks Oko wanda shi ne Mai taimaka masa wajen yada labarai da dabaru, ya bukaci a kama duk wadanda ake zargi.

Gwamnan APC
Gwamnan Ebonyi, David Umahi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Jawabin da Chooks Oko ya fitar

David Umahi ya bada umarnin ayi gaggawar kama Shugaban APC, Stanley Emegha da ‘dan takara, a kan rawar da suka taka wajen kashe mutane uku a Ekoli Edda.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Yi Magana a Kan Wa Za a Dauka Tsakanin Tinubu da Atiku a Katsina

Umahi ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda ya kama duk wadanda ake zargi su na da hannu a wannan aika-aika da aka yi, domin a tabbatar doka tayi aiki a kansu.

- Chooks Oko

A jawabin, Gwamnan Ebonyi ya dakatar da yin duk wani taron jama’a a Ekoli Edda har sai zuwa lokacin da zaman lafiya da kwanciyar hankali su ka dawo.

Tribune ta ce yanzu jami’an ‘yan sanda da sojoji da dakarun Ebubeagu sun zagaye kauyen domin gudun abin da ya faru ya sake maimaita kan shi a nan gaba.

Abin da ya faru - Kwamishinan 'yan sanda

Ana haka ne Kwamishinan ‘yan sanda na Ebonyi, Aliyu Garba ya tabbatar da mutuwar mutane uku a sakamakon tada-zaune-tsayen da aka yi a jihar.

CP Aliyu Garba ya fitar da jawabi a Abakaliki, ya ce rikicin da ya barke tsakanin mutanen Chima Eni da Stanley Emegha ne ya jawo aka rasa rayuka a jihar.

Kara karanta wannan

Yan Daba Sun Kona Gidan Shugaban Jam’iyyar APC a Wata Jahar Kudu

CNPDN sun bi bayan Tinubu

Dazu aka samu labari 'Yan Kungiyar Citizens Network for Peace and Development in Nigeria da su ke tare da Goodluck Jonathan, sun raba jiha da PDP a 2023.

Sakataren kungiyar CNPDN, Mr. Francis Okereke Wainwei ya fadi abin da ya sa za su goyi bayan Bola Tinubu a kan Atiku Abubakar da ke takara a jam’iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng