Yan Baranda Sun Kona Gidan Shugaban Jam’iyyar APC a Ebonyi

Yan Baranda Sun Kona Gidan Shugaban Jam’iyyar APC a Ebonyi

  • Yan baranda sun farmaki shugaban jam'iyyar APC a jihar Ebonyi, Stanley Okoro-Emegha inda suka budewa tawagarsa wuta
  • Da ya ga yan bindigar sun sha kansa da mabiyansa, Okoro-Emegha ya arce zuwa Abakaliki inda su kuma suka kona gidansa da ke Ekoli Edda, a karamar hukumar Afikpo ta kudu
  • Jagoran na APC ya zargi yaran tsohon ciyaman na karamar hukumar Afikpo ta kudu, Eni Chima, da kai masa harin

Ebonyi - Wasu yan daba sun kona gidan shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ebonyi, Stanley Okoro-Emegha, da ke Ekoli Edda, a karamar hukumar Afikpo ta kudu.

Wani da abun ya faru a kan idonsa wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 10:18 na daren ranar Litinin, 26 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Daga Shiga Motar Haya a Titi, An Halaka Matasa 3 Tare da Cire Sassan Jikinsu

Logon APC
Yan Baranda Sun Kona Gidan Shugaban Jam’iyyar APC a Ebonyi Hoto: Punch
Asali: UGC

Wata majiya abun dogaro a yankin ta fadama jaridar Punch cewa Okoro-Emegha, ya yi adawa da zaben wata kungiyar matasa a yankin wacce ta samar da masu biyayya ga tsohon ciyaman na karamar hukumar Afikpi ta kudu, Eni Chima, a matsayin shugabannin kungiyar.

A cewar majiyar, shugaban APCn, ya nuna rashin jin dadinsa kan zaben sannan ya ja hankalin sabon ciyaman na yankin, Hon. Chima Ekumankama, wanda ya soke zaben sannan ya yi kira ga rusa kungiyar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa yan barandan sun budewa jigon na APC da mukarrabansa na Ebubeagu wuta a lokacin da ya ziyarci yanki, kuma sun yi artabu da juna.

Da ya ga cewa yan barandan da ke dauke da AK-47 sun sha garfin jami'ansa na Ebubeagu, sai jigon jam'iyyar ya ja baya sannan ya tafi Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Kara karanta wannan

Dan Sanda Ya Harbe Wata Lauya a Hanyarta Ta Dawowa Daga Coci a Ranar Kirsimeti

Yayin da yake Abakaliki, labarai sun shigo cewa wasu da ake zaton yan daba ne sun cinnawa gidansa wuta.

Martanin yan sanda

Zuwa yanzu ba a samu jin ta bakin yan sandan jihar Ebonyi ba domin basa amsa kiran waya ko sakonnin da aka tura.

Shugaban APCn ya yi martani

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban APCn, Okoro-Emegha, ya ce yan baranda da ke biyayya ga wani dan siyasa a yankin ne suka far masa,yana mai cewa miyagun sun kuma kona gidansa, rahoton Sahara Reporters.

Ya ce:

"Eh da gaske ne. Sun kai mani hari da daddare a garin Ekoli Edda, kuma wadannan mutanen da na sani, na ji yanzu wai sun kona gidana.
"Wadannan yaran Eni ne kuma sun farmakeni sannan sune suka kona gidana. Na kira yan sanda da sauran hukumomin tsaro don su shiga aiki. Sun san abun da za su yi don gano gaskiyar lamarin. Sun san abun yi."

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Bindiga a Kaduna, Sun Kwato Bindigogin AK47 Guda 4

Ba a samu jin ta bakin Chima ba kan lamarin a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

A wani labarin, wani matashi ya horar da mahaifinsa ta hanyar hana shi hawa motarsa saboda ya ki goyon bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party.

Asali: Legit.ng

Online view pixel