Gwamna Ya Manta Sanayya, Ya Lafta Tarar N5m Kan Jam’iyyarsa Saboda Saba Dokar Kamfe

Gwamna Ya Manta Sanayya, Ya Lafta Tarar N5m Kan Jam’iyyarsa Saboda Saba Dokar Kamfe

  • Bai halatta ga wata jam’iyya ta daura fastoci ko allon ‘dan takara a Ebonyi ba tare da izinin gwamnati ba
  • Sabawa wannan doka ya jawo Gwamnatin David Umahi ta ci tarar N5m a kan APC da wasu Jam’iyyun siyasa
  • An ba jam’iyyun nan da karshen Disamba su biya tarar N5m, idan kuwa ba haka ba sai sun yi kashin N50m

Ebonyi Gwamnan Ebonyi ya umarci jam’iyyar APC ta reshen jiharsa da ta biya tarar Naira miliyan 5 a dalilin sabawa doka mai cikakken iko ta 3 ta 2022.

Hukumar dillacin labarai na kasa ta ce Mai girma David Umahi ya samu jam’iyya mai mulki da aikata laifi wajen yakin neman zaben shekara ta 2023.

Doka ta 3 da Gwamnan ya kawo a shekarar bana ta haramtawa jam’iyyun siyasa amfani da wasu wuraren zaman al’umma wajen yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Yi Babban Rashi, Wani Babban Ƙusa a PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

Bai halatta ayi kamfe a makarantu, tashoshin zirga-zirga da kasuwanni ba tare da izinin gwamnati ba.

APC sun karya doka - Gwamnati

Daily Trust ta ce wannan doka da APC ta karya, ta hana jam’iyyun siyasa su daura fastocin neman takara a tituna ko gada sai sun samu izinin gwamnati.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai da wayar da kan al’umma na Ebonyi, Uchenna Orji ya fitar, ta nuna takaici a kan yadda ake sabawa dokar nan.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Ebonyi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Uchenna Orji ya yi magana a garin Abakaliki a ranar 25 ga watan Disamba 2022, ya ce jam’iyyun siyasa su na daura fastocinsu a tituna, gadoji da layin wuta.

Sauran jam'iyyu sun yi koyi da APC

Jaridar Sun ta ce jam’iyun da aka samu sun saba dokar nan sun hada da APC, PDP, LP da APGA.

Kara karanta wannan

Sabuwar kitimurmura: Ba mu san adadin sabbin Naira da aka buga ba, inji CBN

"A lokacin da APC ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da na gwamna a jihar, ta bata wuraren more rayuwa da fastocin ta.
Wannan ya sa saura jam’iyyu su kayi koyi da APC. An bata mafi yawan wurare da fastoci, wanda ya sabawa dokar gwamnato jiha kan fastoci."

- Uchenna Orji

Tarar za ta iya zama N50m

Orji yake cewa Gwamna Umahi ya dauki matakin hukunta jam’iyyarsa ta APC mai mulki domin ya koyawa sauran jam’iyyun hamayya darasi a jihar.

Hakan ta sa aka ci APC tarar N5m, dole a biya tarar ta asusun hukumar karbar haraji, a wallafa risitin a shafukan sada zumunta ko a ci ta ta tarar N50m.

APC ta biya KCTA N1m

An yi irin haka a jihar Kaduna domin kwanakin baya an ji labarin yadda daura fastoci ya jawo Hukuma ta laftawa Jam’iyyar APC mai mulki tarar N1m.

Shugaban hukumar KCTA, Muhammad Hafiz Bayero ya cire sani da sabo, ya aikawa Shugaban APC na reshen jihar Kaduna takarda cewa ya sabawa doka.

Kara karanta wannan

PDP Ta Fallasa ‘Umarnin’ da Bola Tinubu Ya ba ‘Yan APC da Aka Yi Taron Sirri a Landan

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng