Tattalin Arzikin Najeriya Zai Inganta Idan Atiku Ya Lashe Zabe: Primate Ayodele Ya Yi Hasashe
- Babban faston Najeriya, Primate Elijah Ayodele, ya magantu a kan makomar zaben shugaban kasa na 2023
- Malamin addinin ya ce Allah ya sanar da shi wasu zantuka game da yadda za ta kasance a kasar idan kowanne daga cikin manyan masu neman takara ya lashe zabe
- Ya ce a gwamnatin Atiku tattalin arziki zai bunkasa, na Tinubu za a samu ci gaba kadan yayin da gwamnatin Peter Obi talaka zai dara mai kudi kuma zai koka
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana abubuwan da za su faru gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023.
A wata takarda da ya saki a ranar Asabar, 24 ga watan Disamba kuma aka gabatarwa Legit.ng, Primate Ayodele, ya ce abun da ba a zata ba zai faru a siyasar 2023.
Ayodele, wanda ya yi ikirarin cewa bai da kowani dan takara da yake goyon baya cikin masu neman shugabancin kasar, ya ce Allah ya bayyana masa wasu sakonni game da manyan yan takara a zaben.
Yadda abun zai kasance ta kowani bangare
Manyan yan takarar shugaban kasa a zaben sune Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na All Progressives Congress (APC), Atiku Abubakar na Peoples Democratic Party (PDP) da Peter Obi na Labour Party (LP).
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar Ayodele, Allah ya nuna masa cewa idan Atiku ya lashe zaben shugaban kasa, tattalin arzikin Najeriya zai bunkasa inda ya kara da cewar idan Tiunubu ya samu tikitin, Najeriya za ta dan inganta kadan.
Ya kuma bayyana cewa idan Labour Party ta lashe zaben shugaban kasa, zai zama gwamnatin talakawa inda masu kudi za su dunga kokawa.
Primate Ayodele ya ce:
"Allah ya bayyana mani cewa idan Atiku ya lashe zaben shugaban kasa tattalin arzikin Najeriya zai inganta kuma idan dan takarar APC, Tinubu ya samu tikitin, Najeriya za ta dan inganta kadan. Idan Labour Party ta lashe shugabanci, zai zama gwamnatin talakawa inda masu kudi za su ta korafi.
"Gwamnatin PDP za ta kasance na talaka da mai kudi, na manya a karkashin gwamnatin APC amma talakawa ma za su ji dadi da marasa ilimi."
Da wuya Atiku ya kawo kuri'un Kano, an bayyana dalili
A wani labarin kuma, hasashe sun nuna zai yi matukar wahala Atiku Abubakar na PDP ya lashe kuri'un al'ummar jihar Kano a babban zaben 2023.
Dalili kuwa shine kaddamar da Muhammad Abacha da babban kotun tarayya tayi a matsayin sahihin dan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar Kano. Tun farko dai Atiku da kwamitin NWC na PDP basa goyon bayan takararsa.
Asali: Legit.ng