Duniya juyi-juyi: Gwamna Ya Ce Tsohon Gwamna da Yaransa Su Dawo da Motoci 11
- Gwamnatin jihar Osun tayi wani bincike, ta gano tsohon Gwamnanta ya bar ofis da motocin N2.9bn
- A dalilin haka Ademola Adeleke ya bada sanarwar a gaggauta dawo da duk motocin da aka tsere da su
- Ana sa ran Gboyega Oyetola, mai dakinsa da wasu mukarrabansu za su maido motocin da ke hannunsu
Osun - Gwamnatin jihar Osun ta umarci tsohon Gwamna, Gboyega Oyetola ya dawo da motoci 11 da ake zargin ya dauka daga jihar kafin ya bar ofis.
Premium Times a rahoton da ta fitar a ranar Juma’a, 23 ga watan Disamba 2022, ta ce ana zargin Gboyega Oyetola ya tafi da wasu motocin gwamnati.
Baya ga tsohon Gwamna Oyetola, gwamnatin Ademola Adeleke ta ta ce mai dakinsa, Kafayat Oyetola da wasu hadimai sun tsere da dukiyoyin jama’a.
Ademola Adeleke ya bada wannan sanarwa ne ta bakin Mai magana da yawun bakinsa, Olawale Rasheed. Za a samu labarin nan a jaridar This Day.
Motocin N2.9bn sun bar hannun gwamnati
A jawabin Mai girma Gwamnan, ya ce darajar motocin da wadannan mutane da suka bar gadon mulki a watan Nuwamban nan suka dauka ya kai N2.9bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zuwa lokacin da muka tattara rahoton, tsohon Gwamnan na APC, Kafayat Oyetola da mukarraban Oyetola ba su maidawa gwamnati mai-ci martani ba.
Gwamnatin Osun ta ce wani kwamitin da aka kafa domin karbo dukiyoyin jihar da suka bar hannunta ya umarci wadannan mutane su dawo da motocinsu.
An umarci Gboyega Oyetola, Hajia Kafayat Oyetola da duk wadanda suka aiki da gwamnatin da ta shude, su dawo da motocin da ke hannunsu a yanzu.
Kwamiti ya ce an sabawa ka'ida
Kwamitin yana zargin cewa an mallaka masu motocin ne ba tare da an bi doka da ka’ida ba. Za a bukaci a dawo da motocin nan ba tare da bata lokaci ba.
Oyetola na APC ya sha kashi ne a zaben da aka yi a watan Yuli a hannun Ademola Adeleke wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP.
Tun da Ademola Adeleke ya hau mulki, yake bankado abubuwan da ake zargin gwamnati baya ta aikata. Oyetola yana ganin bita-da-kulli ake yi masa.
Wike ya rufe ofishin Atiku
Rahoto ya zo cewa yakin neman zaben Atiku Abubakar a Jihar Ribas ya zama aiki, Gwamnatin Nyesom Wike ta hana magoya bayan ‘Dan takaran sakat.
Gwamnatin Ribas ta fake da wasu dokoki, ta ce a dalilinsu ne aka rufe ofishin da ake yi wa Atiku/Okowa kamfe a zaben shugabancin kasa a garin Fatakwal.
Asali: Legit.ng