Wani Babban Ƙusa a PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Sokoto

Wani Babban Ƙusa a PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Sokoto

  • Jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ta tafka babban rashi inda wani ƙusa ya fice daga cikinta zuwa jam'iyyar APC
  • Tsohon ɗan jam'iyyar ta PDP yace jam'iyyar ta gaza wajen mulkar al'ummar jihar yadda yakamata
  • Ya sha alwashin bayar da dukkanin gudunmawar da ta dace ga jam'iyyar APC domin dawo da jihar kan turbar da ta dace

Sokoto - Wani babban ƙusa a jam'iyyar PDP ta jihar Sokoto, Alhaji Yusha’u Kebbe, a ranar Juma'a ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC.

Kebbe ya sanar da hakan ne a yayin wata ganawa da ƴan jarida a Sokoto, inda ya alaƙanta wannan matakin da ya ɗauka kan rashin jagoranci mai kyau, kasa samar da ababen more rayuwa ga mutanen jihar Sokoto na gwamnatin PDP.

Kebbe
Wani Babban Ƙusa a PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Sokoto
Asali: UGC

Ya bayyana cewa sai da ya tuntuɓi magoya bayan sa a dukkanin ƙananan hukumomi 23 na jihar kafin ya yanke wannan hukuncin na sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC. Jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wa ya kaiku: An gurfanar da 'yan APC da PDP 14 a Borno bisa aikata wani babban laifi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa, da yawa daga cikin magoya bayan na sa sun yarda da cewa ɗan takarar gwamna da PDP ta tsayar yana cikin gwamnati mai ci ne a yanzu, saboda haka ba wani sauyi da zai kawo.

Yace wasu daga cikin magoya bayan na sa sun zaɓi da su bi bayan gwamna Aminu Tambuwal ko kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Wamakko, a matsayin jagoran APC, sai dai yace shi ya zaɓi da ya bi bayan Wamakko.

Kebbe ya nuna ƙwarin guiwa kan cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yana da ƙwarewar da zai shugabanci Najeriya inda ya nuna hakan lokacin da ya mulki jihar Legas.

Dalilin sa na komawa APC

A cewar sa ya koma APC ne saboda niyyar da take da ita wajen dawo da jihar kan turbar da ta dace, inda yace zai bayar da dukkanin goyon bayan da ya dace domin tabbatuwar hakan.

Kara karanta wannan

2023: Abokin Takarar Kwankwaso Ya Faɗi Yuwuwar NNPP Ta Kulla Maja da Wasu Jam'iyyu Nan Gaba

Alhaji Yusha'u Kebbe dai ya taɓa takarar gwamnan jihar Sokoto a zaɓen 2012 da aka sauya a ƙarƙashin jam'iyyar ANPP, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

PDP A Kano: Aminu Wali Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Bayan Kotu Ta Ba Wa Abacha Nasara

A wani labarin kuma ƙorarren ɗan takarar gwamnan PDP a jihar Kano, Aminu Wali ya bayyana cewa zai tafi kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.

Babbar Kotun ta ayyyana Muhammad Abacha a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan jihar Kano karkashin inuwar jam'iyyar PDP a 2023.

Alkalin Kotun mai zama a birnin Kano ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa ta maye gurbin Wali da Abacha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262