Tinubu Zai Lallasa Atiku a Zaben 2023, Inji Malamin Hindu Satguru Maharaj Ji

Tinubu Zai Lallasa Atiku a Zaben 2023, Inji Malamin Hindu Satguru Maharaj Ji

  • Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ne zai lashe zaben 2023, inji Satguru Maharaj Ji
  • Babban malamin addini kuma ma’assasin tafiyar One Love Family ya fadi ne haka ne a ranar Laraba 21 ga watan Disamban 2022
  • Ya kuma ce Tinubu zai ba da abin da ake bukata a Najeriya tare da cewa bai da nuna wariyar addini a harkarsa

A wani hange da malamin addini ya yi, ya hango wanda zai lashe zaben shugaban kasa tsakanin Peter Obi, Atiku Abubakar da Asiwaju Bola Tinubu a 2023.

A cewar ma’assasin tafiyar One Love Family, Satguru Maharaj Ji, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ne zai lashe zaben 2023 da ke tafe, rahoton New Telegraph.

Ya fadi hakan ne a ranar Laraba 21 ga watan Disamba yayin bikin cikarsa shekaru 75 a duniya, inda yace Atiku na PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour ba za su mulki Najeriya ba.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Magantu Kan Jita-Jitar Da Ake Yi Cewa Tinubu Zai Musuluntar Najeriya

Satguru ya hango wanda zai lashe zaben 2023
Tinubu Zai Lallasa Atiku a Zaben 2023, Inji Malamin Hindu Satguru Maharaj Ji | Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

Dalilin da yasa Tinubu ya fi cancanta ya gaji Buhari

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, Tinubu ya fi cancanta ya zama shugaban kasa, kuma tabbas dan takarar na APC bai da keta da nuna wariya ta addini.

Hakazalika, Tinubu ne zai iya gyara gadar alaka tsakanin jama’ar kasar nan ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, NewsDirect ta tattaro.

Ya kara da cewa, a kuma tsarin tafiyar da siyasar kasar nan, yanzu lokaci ya yi da yankin Kudanci zai kawo shugaban kasa na gaba.

A cewarsa:

“Kuma daga Kudu ya fito, kuma abin da ‘yan Najeriya ke cece-kuce a kai shine, yankin Kudanci ya samar da shugaban kasa na gaba.”

Ya kamata Atiku ya mance da batun shugabanci, inji Satguru

Da yake magana game da dan takarar PDP Atiku Abubakar, malamian ya bayyana cewa, maganganun Atiku sun nuna yana da tsarmin kabilanci, tun da a baya yace ‘yan Arewa kada su zabi dan Kudu.

Kara karanta wannan

Bude 'Border': Atiku ya fadi abin da zai yiwa iyakokin kasar nan idan ya gaji Buhari a 2023

Saboda haka, ya yi kira ga Atiku da ya ajiye aniyarsa ta gaje Buhari saboda ceto kasar nan da kuma kiyaye muradin ‘ya’yanta.

A shekarar 2018, Satguru ya taba bayyana goyon bayansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yace zai mara masa baya a zaben 2019.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.