Dalilin da yasa zan goyi bayan Buhari a zaben 2019 Satguru Maharaj Ji

Dalilin da yasa zan goyi bayan Buhari a zaben 2019 Satguru Maharaj Ji

- Da alamu sakar shugaba Buhari za tayi kyau a zabe mai zuwa

- Don tun yanzu wani mai gano abubuwan ban al'ajabi ya goyi bayansa

- Har ma ya nemi sauran 'yan Najeriya da su marawa shugaban kasar baya a zaben 2019

Wani shahararren boka mai gani har hanji Satguru Maharaj Ji ya bayya kudirinsa na goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wani mai gani har hanji, Satguru Maharaj ya goyi bayan Buhari a 2019 saboda wani dalili da ya bayyana
Wani mai gani har hanji, Satguru Maharaj ya goyi bayan Buhari a 2019 saboda wani dalili da ya bayyana

Sannan ya yi kira ga yan Najeriya su sake zabar shugaban kasar a karo na biyu domin kai Najeriya tudun mun tsira, musamman wajen kamalla ayyukan da ya faro tare da kawo karshen cin-hanci da rashawa.

Maharaj Ji ya ce yana goyan bayan shugaba Buhari domin shi ne mutum na farko da yake kokarin ganin ya kawo karshen matsalolin da kasar nan ke fuskanta har ma da Nahiyar Afirka baki daya.

Satguru ya furta hakan ne a yayin jawabin da ya gabatar a lokacin bikin cikar wurin bautar ta su shekaru 38 da kafuwa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotuna

Maharaj Ji ya kara da cewa, yana da kyau a yiwa Buhari gyara ta hanyar nuna inda ake so ya maida hankali domin kawo nagartattun gyare-gyare idan an zabe shi a karo na biyu.

A cewarsa, Buhari ba wai shugaban Hausawa ko Yarbawa ko Inyamurai bane, face shugaban kasar Najeriya baki daya, kuma shi ma haka Shugaba Buharin ya dauki kansa a hakan.

"Abinda muke bukata shi ne, mu mara masa baya, tare da nuna goyon bayanmu a gare shi gami da fito masa da wuraren da muke so ya maida hankali domin kawo gyara, in har muka yi hakan kuma bai gyara ba ina baku tabbacin ni ne mutum na farko da zan fara masa tirjiya". Maharaj ji ya bayyana.

"A halin da Najeriya take ciki muna bukatar shugaba wanda ba ruwansa da nuna kabilance ko bangaranci, muna bukatar shugaban da zai iya ganin matsalolinmu kuma ya karbi kowa a matsayin nasa wannan shi ne abinda muke bukata.”

Maharaj ji dai ya fara bayar da labarun duba na ban mamaki tun yana dan shekara 33 ga duk wadanda suka je neman taimako wurin shi tun a shekarar 1984, daga cikin wadanda ya taimakawa har da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da sauran masu neman dukiya a Najeriya da sauran mutane a fadin duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel