Zaben 2023: Buhari Ya Bayyana Adadin Kujerun Da Jam'iyyar APC Za Ta Lashe
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta APC ne za ta lashe dukkan kujeru a zaben 2023
- Buhari ya kuma ce yana tare da jam'iyyar ta APC kuma a shirye ya ke ya fita yin kamfen a duk lokacin da bukatar hakan ta taso
- Buhari ya kuma ce kawo yanzu kamfen din na APC abin ban sha'awa ne kuma idan an kwatanta da sauran jam'iyyu sun yi musu nisa
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana kyautata zaton cewa jam'iyyar APC ne za ta lashe dukkan kujeru cikin adalci a zaben shekarar 2023.
Shugaban kasar kuma ya bawa jam'iyyar ta APC da yan takararta tabbacin cewa a shirye ya ke ya yi wa dan takarar shugaban kasa da sauran yan takarar kamfen 'da kuzarinsa da niyya mai kyau.'
Buhari zai yi wa Tinubu da sauran yan takarar APC kamfe
Wannan tabbacin a cewar sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu, an yi ta ne don kore damuwar da wasu ke yi na cewa shugaban kasar baya zuwa kamfen tun bayan kadamarwa a jihar Plateau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce duk da cewa shugaban kasar bai yi watsi da harkokin jam'iyya ba, ba zai yi wu kuma ya manta da ayyukansa ba a matsayin shugaban kasa.
Da ya ke magana da yan Najeriya a Washington DC yayin ziyararsa Amurka, Buhari ya jadada cewa a shirya yake kowane lokaci ya fita yin kamfen don nasarar jam'iyyarsa a zaben 2023.
Sanarwar ta cigaba da cewa:
"Shugaban kasar ya lura cewa kamfen din na APC ne mafi karfi a tarihin baya-bayan nan."
'Sun kasance abin ban sha'awa kuma da cikaken karfinsu,' idan aka kwatanta da abokan hammayar da bisa alamu ke kokarin bin sahun su.
"Ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam'iyyar za ta yi nasara a dukkan zabuka cikin adalci da gaskiya."
Gwamna Masari ya magantu kan jita-jitar cewa Tinubu zai musuluntar da Najeriya
A wani rahoton, Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya karyata jita-jitar cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai musuluntar Najeriya.
Masari ya furta hakan ne yayin jawabin da ya yi a ranar Talata, 20 ga watan Disamba, yayin wani taro da kungiyar kiristoci na arewa da matar Tinubu, Sanata Remi Tinubu, a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng