2023: Za Mu Fi Maza Tabuka Abin Azo A Gani, In Ji Yan Takarar Gwamna Mata a Najeriya

2023: Za Mu Fi Maza Tabuka Abin Azo A Gani, In Ji Yan Takarar Gwamna Mata a Najeriya

  • Yan takarar gwamna mata da yar takarar shugaban kasa sun kallubalance takwarorinsu maza kan harkokin mulki a kasar
  • Yan takara da suka yi jawabi mabanbanta sun nuna bukatar da ke akwai na bawa mata dama su jagoranci kasar don suna ganin za su fi mazan iya aiki
  • Yan takarar sun bayyana kallubalen da suka fuskanta yayin da suke kira ga yan Najeriya su mara musu baya a zaben da ke tafe

FCT, Abuja - Yan takarar gwamna mata daga jam'iyyun siyasa daban-daban, a ranar Litinin sun yi alkawarin za su yi aiki fiye da takwarorinsu maza idan an zabe su a yayin zaben 2023 a Najeriya.

Sun kuma soki mafi yawan yan siyasa, musamman gwamnoni saboda gazawarsu na samar da romon demokradiyya ga mutane da suka zabe su, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Darikar Tijjaniya A Nigeria Sun Marawa Bola Ahmed Tinubu Baya

Yan takara mata
2023: Za Mu Fi Maza Tabuka Abin Azo A Gani, In Ji Yan Takarar Gwamna Mata a Najeriya. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yan takarar gwamna matan sun fadi abin da ke zukatansu ne a Abuja yayin wani taro da yan jarida da Women Radio da Women in Business tare da tallafi daga United Nations Women (Nigeria) da Gwamnatin Kanada suka shirya.

Wakiliyar mata na UN, Beatrice Eyong, ta ce duk da cewa yawan mata da ke majalisa ya rubanya a duniya tun 1995 zuwa kashi 26.4 cikin dari, lamarin ba haka yake a Najeriya ba don raguwa ya ke yi tun 1999.

Abin da wasu yan takarar gwamna mata suka ce

Gladys Ngozika Johnson-Ogbuneke

Yar takarar gwamna na jam'iyyar Social Democratic Party a Jihar Abia, Gladys Ngozika Johnson-Ogbuneke rashin gwamnati nagari ne ya janyo zanga-zangar Endarsa a 2020.

Ta kara da cewa mutanen Abia sun shafe shekaru 31 suna shan wahala tun bayan kirkirar jihar, tana mai cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta bawa tsaro da ilimi muhimmanci, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Sheke Tsohuwa Mai Shekaru 120 tare da Wasu 5

Anabel Cosmos

Yar takarar gwamna na jam'iyyar Action Peoples Party a Jihar Delta, Anabel Cosmos, ta jadada bukatar da ke akwai na mata su canja tsarin yadda ake abu a kasar.

A cewarta, rashin kudi ne babban kalubalen da mata ke fama da shi.

Cosmos ta ce:

"Mata na shan wahala, sashin ilimin mu na shan wahala. Da karamin mukamin da aka bani bayan na yi takarar gwamnan Delta a 2019, na yi ayyukan tallafawa mutane a yanki na. Amma na yi shawarar yin canji.
"Kudi muke bukata. Mu tallafawa junan mu. Mata ba su tallafawa junansu. Mu dena karya juna a fili. Muna manajojin gidajen mu, don haka zamu iya kulawa da gidajen mu. Na zo nan don kallubalantar mazan zan fi su iyawa."

Dr Ebiti Ndok-Jegede

Yar takarar shugaban kasa na jam'iyyar r of the Allied Peoples Movement, Dr Ebiti Ndok-Jegede ta ce jam'iyyar ta za ta sake tsarin rabon arzikin kasar idan an zabe ta.

Kara karanta wannan

'Yan PDP Sun Shiga Zulumi, An yi Taron Gangamin Kamfen, Fili a Bushe a Wata Jahar Arewa

Yayin da take jaddada bukatar farfado da masana’antu da suka lalace, ta ce Najeriya za ta ci gaba ne kawai idan yan kasar suka canja tunaninsu kan harkokin mulki.

Matan dan takarar gwamna na YPP da aka tura gidan gyaran hali ta fita yi masa kamfen

A wani rahoton, matar sanata Albert Bassey Akpan, dan takarar gwamna na jam'iyyar Young Peoples Party, YPP, a jihar Akwa Ibom ta fara masa kamfen duk da cewa yana gidan yari.

Kamar yadda The Cable ta rahoto, an fara kamfen din na Akpan ne a ranar 9 ga watan Disamban 2022 a Ekpo tare da abokin takararsa, Asuquo Amba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164