2023: Gwamnan APC a Arewa Ya Yi Amai Ya Lashe, Ya Amince da Bukatar PDP
- Daga karshe dai gangamin yakin neman zaben shugaban kasa, gwamna da sauransu zai gudana kamar yadda PDP ta tsara a Katsina
- Gwamnatin jihar karkashin Aminu Bello Masari na APC ta amince da bukatar PDP na gudanar da taron Atiku a fitaccen filin wasa
- Tun da farko an ji jam'iyyar PDP na sukar gwamna Masari bisa hana su amfani da filin duk da sun nemi hakan har sau biyu
Katsina - Daga karshe dai gwamna Aminu Bello Masari ya amince da bukatar PDP na amfani da shahararren filin wasan Muhammad Dikko wato Karkanda wurin gudanar da ganngamin kamfe.
Alhaji Usman Kankiya, babban Sakataren sashin al'amuran siyasa da ayyukan yau da kullum ne ya tabbatar da haka, kamar yadda jaridar PM news ta rahoto.
A sanarwan da babban Sakataren ya fitar, ya ce:
"Kari kan takaradar mu ta ranar 13 ga watan Disamba, 2022 kuma bayan samun ci gaba a aikin gyaran da gwamnati ke yi a filin wasan Muhammad Dikko, mai girma gwamna Aminu Masari ya sahalewa PDP ta yi amfani da shi a gangamin kamfen da ta shirya ranar Talata."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Tuni dai aka tura wannan amincewa ta gwamna ga kwamishinan wasanni da harkokin walwala domin ɗaukar mataki na gaba."
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jam'iyyar PDP ta soki gwamnatin Masari kan hana ta babban filin da aka fi sani da Karkanda yayin da zata karɓi ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.
A yau Talata, 20 ga watan Disamban, 2022 ake sa ran jirgin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP zai dira Katsinan dikko a ci gaba da yawon tallata manufofin Atiku.
Sai dai ga dukkan alamu rikicin gida dake wakana a jam'iyyar reshen jihar na neman ya shafi kamfen, an tattaro cewa wasu jiga-jigai ba zasu je wurin ba.
Sabon Ciwon Kai Ga Atiku: Jigon PDP Shema Ba Zai Yiwa Atiku Kamfen Ba a Katsina
A wani labarin kuma Tun kafin jirgin Atiku da tawagarsa ya dira Katsina, an ce tsohon Gwamna Shema da magoya bayansa ba zasu je kamfen ba
Tsohon gwamnan, wanda ke da goyon bayan mafi yawan shugabannin PDP a matakin jiha da kananan hukumomi ba ya shiri da ɗan takarar gwamna, Yakubo Lado.
An jima ana rikicin tsakanin bangororin guda biyu a PDP Katsina, sai dai xamu jira muga yadda zata kaya a wurin kamfen Atiku na ranar Talata.
Asali: Legit.ng