Bidiyo Ya Fito Na Yadda Atiku Ke Ganawa da Shugabannin Kiristoci a Kudancin Kaduna
- Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a yanzu haka yana wata ganawa da shugabannin kiristocin Kaduna
- Atiku ya samu rakiyar shugabannin PDP da jiga-jiganta, ciki har da abokin takararsa mai girma gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta
- Mataimakin nasa ne ya tabbatar hakan a rubutun da ya yada a kafar Facebook a ranar Litinin 19 ga watan Disamba
Kafanchan, jihar Kaduna - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya dura jihar Kaduna domin ganawa da shugabannin kiristan yankin.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa,Wazirin Adamawa ya isa yankin Kudancin Kaduna a ranar Litinin 19 ga watan Disamba tare da abokin takararsa, Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta.
Hakazalika, tare dashi akwai jiga-jigan PDP, magoya baya da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.
Duk da cewa Atiku bai bayyana manufar ganawarsa da shugabannin Kirista ba, amma ana kyautata zaton ganawar ba za ta rasa nasaba da tallata kansa gabanin zaben 2023 gare su ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abokin takarar Atiku ya tabbatar da ganawarsu da shugabannin kiristocin Kaduna
Gwamna Okowa ya tabbatar da ganawar Atiku da shugabannin kiristan yankin, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.
A cewarsa:
"Yanzu muka isa Kafanchan domin ganawar masu da tsaki da shugabannin Kirista a Kudancin Kaduna."
Bidiyon da Okowa ya yada ya nuna lokacin da Atiku yake tafe tare da wasu jiga-jigan PDP, sun samu tarba a wurin shugabannin kiristocin yankin na Kafanchan.
APC Ta Caccaki PDP da Atiku Kan Zargin Kullalliya Game da Sunan Tinubu Na Gaskiya
A wani labarin kuma, tawagar gangamin APC da ke tallata Tinubu da Shettima ta bayyana kadan daga abubuwan da dan takarar na shugaban kasa ya tsallake a tsawon lokaci a kasar nan.
Tawagar ta yi martani ne ga magar da PDP ta yada na cewa, akwai wasu batutuwa mara tushe game da aainihin sunan yanka na Bola Ahmad Tinubu.
Ana ci gaba da musayar kalamai tsakanin 'yan siyasar kasar nan tun bayan buga gangar siyasa, a wannan karon ma kamar kullum, ana musayar yawu tsakanin jam'iyya mai ci APC, da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP.
Asali: Legit.ng