Guri/Malam Madori: Tinubu Zai Taimaka Wajen Hako Danyen Mai da Ake da Shi a Arewa
- Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yana kokarin gamsar da mutanen Jigawa su zabu Bola Tinubu
- Da aka je taron yakin neman zaben APC, Gwamnan ya fadi yadda Jihar za ta amfana da mulkin Tinubu
- Badaru ya yi alkawarin gwamnatin tarayya za ta hako danyen man da ke Jigawa idan aka zabi APC
Jigawa - Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa, ya yi kira ga mutanensa da su zabi jam’iyyar APC mai mulki a zabe mai zuwa.
Vanguard ta rahoto Muhammad Badaru Abubakar yana bayanin yadda za su ci moriya idan Bola Tinubu ya dare kan kujerar shugabancin Najeriya.
Mai girma gwamna ya yi wannan kira ne a wajen yakin neman zaben ‘dan takaran Gwamna da jam’iyyar APC mai mulki tayi a garin Malammadori.
A cewar Muhammad Badaru Abubakar, idan Tinubu ya gaji kujerar shugaban kasa, zai taimakawa jihar wajen hako danyen man Guri/Malammadori.
Da aka je taron APC a garin Gumel a karshen watan Nuwamba, Gwamnan ya yi wa mutane alkawarin za a fara hako mai a Jigawa idan APC ta zarce.
Akwai mai a Jigawa?
Rahoton ya ce Gwamna Badaru Abubakar ya yi ikirarin akwai dinbin albarkatun danyen mai a jiharsa, wanda a a iya hako sui dan aka zabi Tinubu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake jawabi ga mutanen karamar hukumar Malammadori a makon jiya, Gwamnan ya yi Allah-wadai da yadda ake lalata allolin takarar APC.
Gwamnan yake cewa ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ba su taba fastocin ‘yan takaran adawa, amma wasuu su na bin fastocin ‘yan takaransu a jihar, su na lalatawa.
Mai girma Badaru Abubakar ya ce za su koyawa jam’iyyun hamayya darasi a zaben badi.
APC ta cika alkawuranta - 'Dan takara
Da ya tashi gabatar da jawabinsa, ‘dan takaran Gwamna a APC, Alhaji Umar Namadi, ya yi alkawarin cigaba daga inda gwamnatin Badaru ta tsaya a Jigawa.
Umar Namadi ya ce zai maida hankali musamman a wajen inganta harkar noma, ilmi da ruwan sha. A cewarsa, APC ta cika alkawuran da ta dauka 2015.
‘Dan takaran da ke neman karbar mulki ya yi kira ga jama’a su zabi APC daga sama har kasa.
Rikicin NNPP a Kaduna
A wata hira da aka yi da Ben Kure, an ji asalin abin da ya sa Shugaban Jam’iyyar na NNPP ya yi murabus bayan tsawon lokaci ana fama da rikicin cikin gida.
Tsohon Shugaban na NNPP yana ganin barinsa Jam’iyya mai alamar kayan marmari ba zai taba takarar shugabancin kasar Rabiu Musa Kwankwaso a 2023 ba.
Asali: Legit.ng