2023: PDP da APC Sun Mutu, NNPP Ce Madadinsu, In ji Kwankwaso
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party ya bukaci masu zabe da su yi waje da APC sannan kada su zabi PDP a zabe mai zuwa
- Sanata Rabiu Kwankwaso ya ayyana NNPP a matsayin madadin jam'iyyun a 2023
- A wata hira da kungiyar Kiristocin Najeriya, Kwankwaso ya jaddada cewar babu abun arzikin da APC da PDP za su tsinanawa yan Najeriya
Kaduna - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Sanata Rabiu Kwankwaso ya yi ikirarin cewa jam'iyyun APC da PDP sun mutu murus, cewa NNPP ce mamadinsu a 2023.
Da yake jawabi a karshen mako yayin wata hira da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihohin arewa 19 da Abuja, a Kaduna, Kwankwaso ya ce APC ta fi PDP muni, jaridar Vanguard ta rahoto.
Kwankwaso ya ce:
"APC ta tabbatar da cewar ta fi PDP muni. Matattun jam'iyyu ne kuma idan akwai wani da ke tunanin za su chanja zuwa na kirki toh imma dai mai shi na yaudarar kansa ko kuma dai yana kulla makirci ne."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwankwaso ya bukaci yan Najeriya da su zabi NNPP a 2023
Ya kara da cewar:
"A babban zabe mai zuwa, kada a yi zabe bisa la'akari da son zuciya wajen zaban wanda zai zama shugaban kasa. A matsayina na Musulmi na goyi bayan tsohon shugaban kasa Oluaegun Obasanjo da Goodluck Ebele Jonatha wadanda suke kiristoci don zama shugaban kasa a kan Buhari.
"Idan akwai wani dan takara da ya fi ni cancanta, zan mara masa baya don ra'ayin kasar. Idan yan Najeriya suka sake yin wani kuskure wajen zaban shugabanni a 2023, mu koka da kanmu kada mu kuka da kowa."
Kwankwaso ya bayyana abun da zai yi a matsayin shugaban kasa
Kwankwaso ya ce, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa, zai sauya tsarin tsaro da kara jami'an tsaro don magance matsalolin tsaro da ke addabar Najeriya.
"Zan ba da fifiko ga bangaren ilimi da aikin yi. Zan samar da tsare-tsare da za su bunkasa tattalin arziki."
A halin da ake ciki, jaridar The Sun ta rahoto cewa Kwankwaso ya nuna kwarin gwiwar cewa za a zabe shi domin jagorantar Najeriya a 2023.
NNPP ta yi sabbin mambobi a jihar Gombe
A wani labarin, mun ji cewa jam'iyyar kayan marmari ta su Kwankwaso ta yi babban kamu a jihar Gombe.
Dan takarar gwamnan NNPP a jihar Gombe, Khamisu Mailantarki, ya tar dubban mambobin jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng