Idan ’Yan Najeriya Suka Kuskura Suka Sake Zaben APC a 2023, Sun Zabi Gallazawa, Inji Primate Elijah
- Duba da abin da Primate Elijah Ayodele ya hango, abubuwa za su cabewa ‘yan Najeriya idan APC ta ci zabe a 2023
- A cewar babban malamin na cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ‘yan Najeriya za su dandana kudarsu idan suka bari APC ta ci gaba da mulki
- Ya kuma bayyana cewa, Atiku da Peter Obi suka bari Tinubu ya karbi ragamar kasar nan, to kasar nan birkicewa za ta yi
Najeriya - Idan jam’iyyar APC ta samu nasa a zaben 2023, ‘yan Najeriya za su shiga wahalar da ta fi ta yanzu, inji Primate Elijah Ayodele, PM News ta ruwaito.
Babban malamin na addinin kirista ya bayyana wannan hangen nasa ne a ranar Lahadi 18 ga watan Disamba, inda ya shawarci ‘yan Najeriya su nesanta kansu da APC.
A fadinsa, jam’iyyar mai ci a shirye take don yin duk mai yiwuwa domin ganin ta ci gaba da mulkin kasar nan da gallazawa ‘ya’yanta.
Primate ya kuma yi ikrarin cewa, APC na yin ruwa da tsaki don ganin ta ci gaba da mulki ba tare da la’akari da halin da ‘yan kasar nan za su shiga ba.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Atiku da Peter Obi su tashi tsaye don hana APC nasara, inji babban malamin coci
Ya kuma yi imani da cewa, idan jam’iyyar PDP ta su Atiku da jam’iyyar Labour ta su Peter Obi suka bari APC ta lashe zaben 2023, to tabbas ‘yan Najeriya za su ci gaba da dandana kudarsu ne kawai, rahoton Daily Independent.
A kalamansa:
“‘APC na son yin nasara a zaben shugaban kasan 2023 ta kowace hanya; ta hanyar fasaha, kudi, bin ka’ida, ba bisa ka'ida ba, ta juyar da tunani, addini da duk abin da za su iya domin samun nasara.
“A shirye suke suka kashe ko nawa ne domin su yi nasara, sun matsu su ci zaben nan. Basu damu ba, ko meye zai faru, su dai kawai su ci zabe ko ta halin kaka.
“APC a shirye take ta ji da duk wanda ya kalubalance ta, a shirye suk tsaf a wannan zaben da duk abin da suke dashi, suna son su yi komai da za su iya. Suna son tafiya nisan zango domin su ci zaben shugaban kasa a 2023.
Dama 'yan Najeriya na ci gaba da nuna damuwa game da yadda Tinubu ke yawan katobara a magana duk sadda ya samu dama.
Asali: Legit.ng