Har Yanzu Muna Tattaunawa: Melaye Da Wasu Yan PDP Sun Yi Watsi Da Rade-radin Cewa Gwamnonin G5 Na Bayan Tinubu
- Masu biyayya ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar sun yi martani kan rade-radin cewa Gwamna Wike ya hade da Bola Tinubu na APC
- Ana ta hasashen cewa gwamnan Ribas ya yanke shawarar goyon bayan Tinubu bayan sun raba gari da Atiku kan Ayu
- Sai dai kuma, Sanata Dino Melaye ya ce Wike ba zai koma kowace jam'iyya ba, yana mai cewa ana kokarin yin sulhu
Duk da rikicin cikin gida da suke fama da shi, masu biyayya ga Peoples Democratic Party (PDP) sun yi watsi da rade-radin cewa akwai yiwuwar Gwamna Nyesom Wike ya juyawa jam'iyyar baya gabannin zaben 2023.
Babbar jam'iyyar adawar ta yi martani ne ga rade-radin cewa gwamnan na jihar Ribas da takwarorinsa hudu da aka fi sani da Gwamnonin G5 sun yanke shawarar marawa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu baya.
Gabannin babban zaben 2023, Wike da takwarorinsa Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na Benue, Okezie Ikpeazu na Abia da Ifeanyi Unguwanyi na Enugu sun bayyana cewa ba za su marawa Atiku baya ba idan shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, bai sauka ya baiwa dan kudu kujerarsa ba.
Wike ya yanke shawarar goyon bayan Tinubu?
Biyo bayan rashin kawo karshen rikicin PDP, ana rade-radin cewa Gwamna Wike ya yanke shawarar goyon bayan Tinubu, ganin cewa ya fi dan takarar Labour Party, Peter Obi karfi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar Punch ta rahoto wasu majiyoyi na cewa Wike zai ci gaba da kasancewa mamba a PDP amma dai Tinubu zai nemawa goyon baya a Ribas.
Wike ba zai iya komawa wata jam'iyya ba, Melaye ya yi martani
Da yake martani, kakakin kwamitin yakin neman zaben Atiku, Dino Melaye ya yi watsi da batun sauya shekar Wike zuwa wata jam'iyya.
Tsohon sanatan ya kuma bayyana cewa ana nan ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu.
"Har yanzu muna magana kuma shi (Wike) ba zai sauya sheka ba," in ji Melaye.
Da yake martani, daraktan dabarun sadarwa na kwamitin kamfen din PDP, Dele Momodu, ya ce zai yi martani da zaran Gwamna Wike ya fito fili ya bayyana matsayinsa kan lamarin.
Momodu ya kuma ce bai san komai ba game da shirin gwamnan na yin hadaka da tawagar dan takarar shugaban kasa na APC.
Asali: Legit.ng