Tsohuwar Abokiyar Gabar Bola Tinubu Ta Bayyana Halin Lafiyar ‘Dan Takaran APC
- Jita-jitar da wasu ke yawo da ita a game da rashin lafiyar Asiwaju Bola Tinubu ba gaskiya ba ce
- Shugaba a kwamitin PCC, Uju Ken-Ohanenye ta ce garau ‘Dan takaran shugaban kasansu yake
- ‘Yar siyasar ta ce idan aka duba irin aikin da yake yi, Tinubu ya fi wasu matasa koshin lafiya
Abuja - Mrs Uju Ken-Ohanenye ta fadawa ‘yan Najeriya suyi watsi da rade-radin da ake yadawa cewa Asiwaju Bola Tinubu bai da cikakkiyar lafiya.
Vanguard ta rahoto Uju Ken-Ohanenye tayi wannan kira a lokacin da ta zanta da hukumar dillacin labarai na kasa a wajen taron NCWD a garin Abuja.
Mataimakiyar shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ta ce maganar cewa Bola Tinubu bai da lafiya, ba ta da tushe ko makama.
Ken-Ohanenye wanda ita kadai ce mace da ta nemi tikitin takarara shugaban kasa a jam’iyyar APC a 2023, ta ce Tinubu ya fi mutane da-dama koshin lafiya.
Tinubu garau yake - Ken-Ohanenye
“Duk kamannin kuruciyar da mafi yawan mu muke da ita, Tinubu ya fi da yawanmu karfi, matasa da yawa ba su da irin karfin da yake da shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babu yadda mutumin da bai da lafiya zai rika shiga can – ya fita can, da watakila yanzu yana gadon asibiti, amma kullum Tinubu yana nan da can.
Bai ma barci a kwanakin sai can cikin dare, yana ta taro, yana magana da mutane, yana canza rayuwar jama’a, amma wasu na cewa bai da lafiya.
Mafi yawan lokuta idan mun fita kamfe, yana nan, wasu lokutan ya kan isa kafin ranar domin ya yi zama da al’umma ana gobe za ayi gangamin."
- Uju Ken-Ohanenye
An rahoto Ken-Ohanenye ta ce da zarar an gama kamfe, Tinubu zai kama hanya zuwa wajen wani taron yakin neman zaben, hakan ya nuna lafiyarsa.
A jawabinta, jigon ta jam’iyyar APC ta ce Tinubu zai ba marada kunya, domin ‘dan takaran yana cikin koshin lafiya, yana ji da karfi tamkar ingarman doki.
Shekaru 30 da kafa NCWD
‘Yar siyasar tayi jawabi wajen bikin cikar cibiyar NCWD shekara 30 a Duniya, inda aka yi amfani da wannan dama aka tara gudumuwa na musamman.
NAN ta rahoto Ken-Ohanenye tana cewa a masu neman zama shugaban kasa, Tinubu ya fi dacewa domin bai duba addini ko kabila sai cancantar mutum.
'Dan hakkin da ka raina shi yake tsone maka ido
Rahoton da muka fitar a makon nan ya nuna cewa a zaben 2023 akwai wandanda za su zabi irinsu Hamza Al-Mustapha a maimakon APC, PDP, LP ko NNPP.
Omoyele Sowore mai shekara 51 da Farfesa Imumolen Christopher mai takara a jam’iyyar Accord Party su na da masu goyon bayansu a zaben da za ayi.
Asali: Legit.ng