Obi: Shugabar Jam’iyyar da Ake Zargi Ta Na Yi Wa PDP Aiki, Ta ‘Sulale’ da Kudin Kamfe

Obi: Shugabar Jam’iyyar da Ake Zargi Ta Na Yi Wa PDP Aiki, Ta ‘Sulale’ da Kudin Kamfe

  • Shugabannin Jam’iyyar Labour Party a Jihar Taraba sun dakatar da Shugabarsu, Esther Gulum
  • Ana zargin Esther Gulum da karkatar da kudi, zagon-kasa da gudanar da jam’iyya da ‘yanuwanta
  • Shugabar da aka dakatar daga ofis na watanni 6 ta ce zargin da ake yi mata ba gaskiya ba ne

Taraba - Jam’iyyar Labour Party (LP) ta reshen jihar Taraba, ta dakatar da Esther Gulum daga kujerar shugaba saboda zargin karkatar da wasu kudi.

Jaridar nan ta The Guardian ta kawo labari cewa ana zargin Esther Gulum tayi gaba da N21m daga cikin kudin da aka ware domin yakin zaben LP a Taraba.

Shugabannin jam’iyyar hamayyar na reshen jihar sun nuna ba su gamsu da jagorancin Gulum ba.

Sakataren gudanarwa na LP a Taraba, Peter Philip ya ce dakatar da shugabar ta su ya zama dole domin a iya gudanar da bincike na musamman a kan ta.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Kai Kamfen Dinsa Filato, Ya Yi Alkawarin Dawo Da Zaman Lafiya Da Farfado Da Tattalin Arziki

Ana mulkin 'yanuwa da dangi

Baya ga zargin karkatar da kudin neman zabe, rahoton ya ce ana tuhumar Gulum da yin watsi da sauran abokan aikinta, tana gudanar da jam’iyya ita kadai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugabannin LP sun ce daga Esther Gulum sai ‘yanuwanta suka san abubuwan da ake yi a jam’iyya, don haka aka ga bukatar a dauki mataki a kan ta.

Peter Obi
Yusuf Datti Baba Ahmad da Peter Obi a Kogi Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Bugu da kari, ana zargin shugabar da yi wa jam’iyyarta zagon-kasa, tana yi wa Gwamnatin Taraba a karkashin jagorancin Darius Ishaku aiki a boye.

Ni 'Yar Obidient ce - Gulum

Amma Gulum ta karyata wadannan zargi da ake yi mata, tun daga rashin gaskiya, zuwa tafiyar da al’amuran jam’iyya tare da ‘yanuwanta da danginta.

Gulum take cewa N17m aka amince za ayi amfani da su wajen gangamin jam’iyya a jihar, kuma an fitar mata da N9m wanda tuni ta ba ‘yan majalisarta.

Kara karanta wannan

'Yan PDP Sun Shiga Zulumi, An yi Taron Gangamin Kamfen, Fili a Bushe a Wata Jahar Arewa

Da take kare kanta, ta ce kuma ba gaskiya ba ne zargin ta da ake yi, da yi wa jam’iyya zagon-kasa ko kuma shigo da danginta wajen gudanar da shugabanci.

“Shirme ne kuma karya ce ka ce kwamitin yakin neman zaben Peter Obi ya bani N20m kuma na batar da su. Ba a bani N20m ba.
N9m kurum aka bani, kuma nayi amfani da su yadda ya kamata, kuma akwai hujjoji.

- Esther Gulum

An ba Tinubu motoci 100 a Neja

Labari ya zo cewa Sanatan Neja ta Gabas, Sani Musa ya yi wa kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu kyauta mai ban mamaki a wajen taron kamfen APC.

Motoci 100 da ofishin kamfen aka ji ‘Dan majalisar ya bada kyauta, shi ma Jigon APC, Muhammad Idris Malagi ya bada kyautar ofishin da za ayi kamfe a Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng