Jiga-Jigan Jihohin Arewa Da PDP Ba Ta Taɓa Samun Nasara Ba Tun 1999

Jiga-Jigan Jihohin Arewa Da PDP Ba Ta Taɓa Samun Nasara Ba Tun 1999

  • Jam'iyyar PDP ta mamaye siyasar Najeriya bayan dawowar Demokuraɗiyya a 1999 kuma ita ta ja ragamar jihohi 31 cikin 36 zuwa Mayun 2007
  • Sai dai duk da cin zamanin da ta yi a wancan lokaci akwai wasu manyan jihohin arewa biyu da ba ta taɓa samun nasara ba har zuwa yau
  • A halin yanzun reshe ya juye da jam'iyyar PDP wacce ta yi ƙaurin sunan zama jam'iyya lamba ɗaya a nahiyar Afirka, ta koma tsagin adawa

Najeriya ta koma Mulkin Demokuradiyya a shekarar 1999 kuma jam'iyyar PDP ce a tarihi ta mamaye siyasar ƙasar a wancan lokaci.

A 2007, PDP ta yi wa kanta kirarari da jam'iyya mafi girma a nahiyar Afirka kuma ta ƙara da cewa zata ci gaba da juya akalar mulkin Najeriya zuwa aƙalla shekaru 60.

Kara karanta wannan

2023: Babu wani Tinubu ko Atiku, ni zan lashe zaben 2023, Kwankwaso ya hango wani haske

Jam'iyyar PDP.
Jiga-Jigan Jihohin Arewa Da PDP Ba Ta Taɓa Samun Nasara Ba Tun 1999 Hoto: officialpdp
Asali: Facebook

Jerin jihohin PDP ta lashe a Najeriya

The Cable tace a Mayu, 2007, PDP ta samu nasarar kafa gwamnati a jihohin Najeriya 31 wanda ya haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Benuwai, Abiya, Bayelsa, Anambra, Edo, Delta, Ebonyi da Kuros Riba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran jihohin sune, Jigawa, Ekiti, Imo, Enugu, Gombe, Nasarawa, Katsina, Kogi, Kaduna, Kebbi, Kwara, Filato, Ogun, Oyo, Ondo, Ribas, Osun, Zamfara, Sokoto, Neja da kuma Taraba.

Jihohin da PDP ba ta taɓa mulka ba tun 1999

Duk da karfin da PDP ke da shi a wancan lokaci, jam'iyyar ba ta taɓa samun nasarar kafa gwamnati ba a jihohin Borno da Yobe dake arewacin Najeriya.

Jam'iyyar ANPP wacce ta rushe zuwa cikin ƙwancen da ya samar da APC ce ke jan ragamar shugabanci a jihohi biyun tun farko.

Haka zalika ana hasashen PDP ba zata iya taɓuka komai ba a jihohin biyu a zaɓen 2023 dake tafe duba da yanayin siyasar da ake yi a jihohin.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Samu Sabon Sumfurin Shugaba Buhari, Doguwa Ya Jaddada Wanda Ya Dace da Mulki a 2023

Ko da an jingine batun cewa APC ce ke rike da mulkin jihohin, jam'iyya mai mulki tana da fitattun ƙusoshi a Borno da Yobe, waɗanda zasu taka muhimmiyar rawa a zaɓe.

Meyasa PDP ka iya shan ƙasa a Borno da Yobe?

Alal misali idan muka ɗauki jahar Yobe, ta samar da shugaban majalisar dattawan Najeriya. Duk da Lawan bai samu tikitin komawa ba amma PDP ba zata iya ikirarin tana da katabus ba a jihar.

Haka a Borno, abokin gamin Bola Tinubu watau Sanata Kashim Shettima daga jihar ya fito, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Tarihin Shettima a matsayin gwamna da Sanata ba zai dusashe ba kuma damarsa ta kawo kuri'un jihar ga APC na da ƙarfi.

A wani labarin kuma Ɗan Takarar shugaban kasa na APC yace idan Allah ya zo ba zai ba 'yan Najeriya kunya ba idan ya lashe zaben 2023

Kara karanta wannan

"Ku Taimaka Ku Zabi APC Sak a 2023" Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Roki 'Yan Najeriya

A wurin gangamin yakin neman zaɓen APC da ya gudana a Kaduna ranar Talata, Tinubu ya sha alwashin kakkaɓe yan bindiga daga doron ƙasa.

Tsohon gwamnan Legas ɗin ya yaba da dumbin ayyukan da Malam Nasiru El-Rufai ya zuba mazauna Kaduna, ya roki su zabi Uba Sani a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel