Mun Samu Sabon Shugaba Buhari a Jikin Bola Tinubu, Ado Doguwa
- Alhassan Ado Doguwa yace Najeriya ta samu sabon sumfurin shugaba Buhari a jikin Bola Ahmed Tinubu
- Shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai yace Buhari ya kawo ci gaba amma zangon mulki biyu ya yi kaɗan a gyara abinda PDP ta ɓata
- A cewarsa, Tinubu mutum ne mai tunani da hangen nesa kuma yana alaƙa da kasashen duniya
Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan tarayya, Alhassan Ado Doguwa, a ranar Talata ya kwatanta ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, Bola Tinubu, da wani sumfurin shugaba Buhari.
Doguwa, yayin da ya bayyana a shirin Politics Toaday na Channels TV, yace Buhari ya cimma nasarori a ɓangaren ilimi da tsaro amma shekaru Takwas sun yi kaɗan ya gyara komai.
Ɗan majalisar ya ce:
"Idan muka ɗauki batun Ilimi, tun daga matakin kasa zuwa manyan makarantu, mun samu gagarumin ci gaba a wannan ɓangaren. Maganar gaskiya ita ce Buhari ba zai iya gyara komai a lokaci ɗaya ba."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
"Shekaru Takwas sun yi ƙaranci ya saita komai da jam'iyyar PDP ta lalata a lokacin mulkinta, muna bukatar fiye da wa'adi ɗaya ko biyu mu gama ayyukan da muka fara."
"Kuma a zahirin gaskiya yanzu kun samu wani sabon Buhari, kuna da gwarzon kulla dabaru, ku na da Uban gida wajen iya tsare-tsare."
Doguwa ya bayyana mai neman zama shugaban kasa da, "Wani mutum mai hangen nesa tun kan ta zo," tare da kyakkyawar alaƙa a kasashen duniya kuma gwamna abin koyi a Legas.
Wane ci gaba Buhari ya kawo a ɓangaren tsaro?
Da yake jawabi kan yanayin tsaron ƙasa, Doguwa yace an samun ci gaba bakin gwargwado karkashin mulkin Buhari, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa idan ka ɗauki shiyyar arewa maso yamma, wasu daga cikin abubuwan da za'a duba sun haɗa da yawan al'umma, matakin ilmin da kuma cuɗanya.
"Amma ina baku tabbacin mun kere tsara a matakin ba da ilimi, kamar jihata watau Kano mun samu gwamna wanda ya ayyana ilimin Firamare da Sakandire kyauta kuma dole."
Babu Wata Matsala Tsakani Na Da Atiku, Gwamna Wike Ya Faɗi Inda Matsalar Take a PDP
A wani labarin kuma Gwamna Nyesom Wike Yace ba wani sulhu da zai shiga matukar Ayu ne a matsayin shugaban PDP na ƙasa
Da yake jawabi ranar bikin cikarsa shekara 55 a duniya, gwamnan Ribas yace a karan kansa ba shi da wata matsala da Atiku Abubakar, mai neman zama shugaban ƙasa a 2023.
Wike yace duk wannan fafutukar yake burinsa kawai a gyara kuskuren da aka tafka kuma a cewarsa bai yi nadamar neman takarar shugaban ƙasa ba.
Asali: Legit.ng