Tinubu Ya Isa Filin Wasan Ahmadu Bello a Kaduna Don Kaddamar da Kamfen Dinsa Na Arewa Maso Yamma
- Yayin da jam’iyyar adawa ta PDP ta ci gaba da damalmalewa da rikicin cikin gida, APC kuwa na can sai tallata dan takarar na shugaban kasa take
- Bola Ahmad Tinubu na APC ya tara tawagar gangaminsa a jihar Kaduna, inda ake kaddamar kamfen APC a Arewa maso Yamma
- A ziyarar Tinubu ta Kaduna, zai zarce Birnin Gwani domin jajantawa wadanda rikicin ‘yan bindiga ya shafa a yankin
Jihar Kaduna- Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya dura filin wasanni na Ahmadu Bello don kaddamar da gangamin kamfen dinsa a yankin Arewa masu Yamma a Najeriya.
Ya dura filin wasannin ne tare da gwaman jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da dan takarar gwamnan jihar a zaben 2023 a APC, Sanata Uba Sani, The Nation ta ruwaito.
PDP Ta Ɗau Zafi, Wike Da Wani Gwamnan Arewa Sun Yi Watsi da Atiku Yayin da Suka Ci Karo a Filin Jirgi
Sauran wadanda ke tare da Tinubu sun hada da gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Abubakar Badaru na jihar Jigawam, Atiku Bagudu na jihar Kebbi da Simon Lalong na jihar Filato.
Manufar zuwan Tinubu Arewa maso Yamma da yiwuwar nasararsa a zaben 2023
Joe Igbokwe, jigo a jam’iyyar APC ya yada hotunan lokacin da Tinubu ya iso filin taron a Kaduna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Nasarar da Tinubu zai samu a yankin Arewa maso Yamma ne zai zama ma’aunin nasararsa a zaben 2023 mai zuwa.
Wannan kuwa zai faru ne saboda yankin Arewa na da ‘yan takara daga yankinsu, kuma Tinubu dai dan yankin Kudu maso Yamma ne.
Bisa al’ada, yankin Arewa ne ke iya zama ma’aunin nasara ga kowane dan takarar shugaban kasa, yanzu ma kusan haka ne a 2023.
Mambobin APC sun koma PDP a jihar Nasarawa
Yayin da ake ci gaba da kamfen, mambobin jam'iyyar APC kusan 10,000 ne suka bayyana sauya sheka zuwa hjam'iyyar PDP a jihar Nasarawa.
Wannan na iya zama barzana ga nasarar Bola Ahmad Tinubu yayin da ake fuskantar babban zaben 2023 mai zuwa nan da watanni uku kacal.
Atiku ABubakar, dan takarar shugaban kasa a PDP ne ya karbi wadannan sabbin mambobi, inda ya yi musu alkawura masu daukar hankali.
Atiku ya ce 'yan Najeriya sun gaji da mulkin APC a matakin kasa da jihohi.
Asali: Legit.ng