Kwankwaso Ya Yi Kus-Kus da Wani ‘Dan Takaran 2023, Ya bar Magoya-baya a Duhu

Kwankwaso Ya Yi Kus-Kus da Wani ‘Dan Takaran 2023, Ya bar Magoya-baya a Duhu

  • Farfesa Peter Umeadi ya kai ziyara ta musamman zuwa gidan Rabiu Musa Kwankwaso a garin Abuja
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar da haduwarsu da ‘dan takaran shugaban kasar na APGA
  • ‘Dan takaran na NNPP ya nuna ya ji dadin zama da Umeadi, zuwa yanzu ba a san sirrin tattaunawarsu ba

FCT, Abuja – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso mai takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, ya hadu da Farfesa Peter Umeadi.

Rabiu Musa Kwankwaso a wani jawabi da ya fitar a shafinsa na Twitter, yace ya zauna da Farfesa Peter Umeadi a gidansa da yake birnin tarayya Abuja.

Peter Umeadi shi ne ‘dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APGA a zaben 2023.

A jawabin ‘dan siyasar ya fitar a cikin tsakiyar dare, bai yi cikakken bayanin abin da aka tattauna ba, hakan ya sa ya bar magoya bayansa a cikin duhu.

Kara karanta wannan

Ina Tinubu Ya Ga Kafasitin Da Zai Mulki Nigeria, Yaje Ya Huta Kawai Inji PDP

Jawabin Rabiu Musa Kwankwaso

"A daren nan, na samu damar karbar bakuncin takwarana, ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA), Prof. Peter Umeadi a gidana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na godewa Farfesa Peter Umeadi da ziyarar, yayin da muke cigaba da kokarin ganin an kafa sabuwar Najeriya. – RMK."
Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a Ekiti Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Neman kuri’un Ibo

Wasu suna ganin akwai yiwuwar ‘dan takaran ya hada-kai da jam’iyyar hamayya ta APGA domin samun kuri’un mutanen Kudu maso gabashin Najeriya.

Jam’iyyar APGA ta fi karfi a Kudu maso gabas, yanzu haka tana rike da mulkin jihar Anambra.

Ziyara zuwa Kasar Yarbawa

Kafin haduwar Kwankwaso da Peter Umeadi, ya ziyarci Kudu maso yammacin Najeriya, ya bude ofisoshin yakin neman zaben jam’iyyarsu ta NNPP.

A sanadiyyar ziyarar ne, tsohon Ministan ya hadu da Sarakuna irinsu Dejin Akure, Aladetoyinbo Ogunlade Aladelusi da Sarkin Ikare, Oba Saliu Akadiri.

Kara karanta wannan

Yadda Mata da Mijinta Su Ka Kusa Shiga Takarar Kujerar Majalisar Dattawa Tare

Tawagar NNPP ta kai ziyarar ban-girma zuwa fadar Oba Adeyemo Adejugbe Aladesanmi II da Oba Jimoh Oyetunji Olanipekun Larooye a Yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng