El-Rufai, Ganduje, da Gwamnoni 5 da ba za su Nemi Kujerar Sanata Bayan Barin Ofis ba
- Gwamnoni da-dama su na sha’awar zama Sanatoci muddin sun ga wa’adinsu a mulki ya zo karshe
- Majalisar Dattawan Najeriya cike take da ‘yan siyasan da sun taba rike kujerar Gwamna a jihohinsu
- Amma akwai daidaikun Gwamnonin da ba su harin kujerar Majalisar Dattawa a karshen mulkinsu
Wannan rahoto na Legit.ng Hausa ya tattaro sunayen Gwamnoni masu barin-gado da ba su neman takarar Sanata a a zaben 2023 dauke da karin bayani.
Su wanene Gwamnonin nan?
1. Nasir El-Rufai
Gwamna Nasir El-Rufai ba zai yi takarar Majalisa a zaben 2023 ba, yana goyon bayan tsohon Kwamishinansa, Muhammad Sani Abdullahi ya maye gurbin Sanata Uba Sani.
2. Abdullahi Umar Ganduje
Da farko kamar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai nemi tikitin Sanatan Kano ta Kudu, amma ya hakura, ya bar Sanata mai-ci, Barau Jibril ya sake yin takarar kujerar a APC.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
3. Ifeanyi Okowa
Mai girma Gwamnan Delta bai cikin masu harin Majalisar da ya bari a 2019, Ifeanyi Okowa shi ne abokin takaran Atiku Abubakar a karkashin PDP a zaben shugaban kasa.
4. Muhammad Badaru Abubakar
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yana cikin Gwamnonin da suka je neman tikitin takarar shugaban kasa, bai nuna yana sha’awar takarar majalisar dattawa a inuwar APC ba.
5. Aminu Bello Masari
Gwamnan jihar Katsina yana ganin cewa ya kamata ya yi ritaya da siyasa a 2023. Duk da ya taba rike majalisar wakilai, Aminu Bello Masari ba zai nemi zuwa majalisar dattawa ba.
6. Udom Gabriel Emmanuel
Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel ba zai nemi Sanata a 2023 ba, Gwamnan ya bada karfi wajen samun tikitin shugaban kasa ne a PDP, a karshe bai iya yin nasara ba.
7. Nyesom Wike
A karshen jerin na mu akwai Gwamna Nyesom Wike na Ribas wanda ya zo na biyu a zaben gwanin ‘dan takarar shugaban kasa a PDP, Wike tun can yace bai harin Sanata a 2023.
El-Rufai: Ba zan iya aikin majalisa ba
An samu rahoto cewa Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai yace bai sha’awar aikin Majalisar Tarayya kamar yadda wasu abokan aikinsa ke yi.
Nasir El-Rufai mai shirin barin mulki yana ganin zama Sanata ya fi wahala a kan wanda ke aiki a bangaren zartarwa, inda Gwamna yake da wuka da nama.
Asali: Legit.ng