Tinubu Ya Dira Kaduna Don Taron Yakin Neman Zabe Ranar Talata

Tinubu Ya Dira Kaduna Don Taron Yakin Neman Zabe Ranar Talata

  • Yayinda jam'iyyar adawa ta PDP ke cigaba da fama da rikice-rikicen cikin gida, jam'iyyar APC na cigaba da kamfenta
  • Dan takarar kujerar shugaban kasan jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya dira jihar Kaduna don taron kamfe
  • Dirarsa ke da wuya, Tinubu ya garzaya karamar hukumar Birnin Gwari, garin da yan bindiga suka addaba

Kaduna - Mai neman kujerar shugaban kasar Najeriya karkashin inuwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya dira jihar Kaduna don kaddamar da yakin neman zaben yankin Arewa maso yamma.

Tinubu ya isa Kaduna ne ranar Litinin, 12 ga watan Disamba, 2022.

Dan takaran ya samu rakiyar abokin tafiyarsa, Sanata Kashim Shettima; Dirakta Janar na kamfen kuma gwamnan Plateau, Simon Lalong; Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje; Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa za mu zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa – Kiristocin Kudu

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, tare da dan takaran gwamnan APC na jihar, Sanata Uba Sani suka tarbesu a filin tashin jirgin saman jihar, rahoton Channelstv.

Tinubu
Tinubu Ya Dira Kaduna Don Taron Yakin Neman Zabe Ranar Talata Hoto: The Governor of Kaduna State
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya tafi gari mai hadari, Birnin Gwari

Dirarsa ke da wuya, tsohon gwamnan na Legas ya garzaya karamar hukumar Birnin Gwari, daya daga cikin garuruwan da yan bindiga suka addaba a jihar.

Ya tafi ziyartar iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Ya samu rakiyar Gwamna Nasir El-Rufa'i, Sanata Uba Sani, da sauran mambobin kwamitin yakin neman zaben jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel