Zan gyara lamarin ASUU, zan biya musu dukkan bukatunsu idan ga gaji Buhari, inji Atiku

Zan gyara lamarin ASUU, zan biya musu dukkan bukatunsu idan ga gaji Buhari, inji Atiku

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP ya bayyana kadan daga abin da ya tanada bayan zaben 2023
  • Atiku ya ce zai warware dukkan rikicin ASUU, musamman batun da ya shafi albashin ma'aikata da ake ciki
  • Atiku ya sha bayyana alkawuran warware matsalolin da Najeriya ke ciki tun bayan fitowarsa takara

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi alkawarin biyan dukkan bukatun kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU idan aka zabe shi a zaben 2023.

Ya ce zai yi kokarin biyansu dukkan albashin da suke bin gwamnati ba tare da bata lokaci ba sabanin yadda gwamnatin Buhari ta yi a yanzu, Channels Tv ta ruwaito.

Duk da cewa kungiyar ASUU ta shafe watanni 8 tana yajin aiki, ta janye yajin tare da jiran tsammani daga gwamnatin Buhari kan batun biyan mambobinta albashi, amma hakan ya ci tura.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Sau 5 Ina Zama da Gwamna Wike, Atiku Abubakar Ya Fallasa Inda Matsalar Take

Atiku ya yi alkawarin warware bashin albashin da ASUU ke bin gwamnati
Zan gyara lamarin ASUU, zan biya musu dukkan bukatunsu idan ga gaji Buhari, inji Atiku | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Mafitar da Atiku yake shirin kawowa

A nasa jawabin a wata tattaunawa da aka shirya, Atiku ya ba kungiyar kwadagon tabbacin cewa, zai warware lamarin albashin da ASUU ke bin gwamnati.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Atiku:

“Zan kara adadin kasafin kudade (a fannin ilimi) sabanin yadda ake bayarwa a yanzu, babu shakka saboda ni nayi imani kuma ina riko da tafarkin ilimi.”

Atiku ya kuma bayyana kukan cewa, yayin da gwamnatin tarayya ta saki kudi ga jami’o’in kasar nan, kudaden ba sa isa ga jami’o’in kai tsaye.

Kudin malaman jami’a ba ya isa garesu kai tsaye

A cewarsa, ana murda kudaden ne zuwa wasu bangarori na gwamnatin tarayya kafin su samu damar zuwa ga wadanda suka dace a jami’o’in kasar nan.

Da yake magana game da mafita, ya ce ya kamata a dakile hakan tare da mika kudaden da suka shafi jami’a ga cikinta kai tsaye, Pulse ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Atiku ya kuma tuna cewa, a lokacin da suke mulkin kasar nan, gwamnatinsu tsakanin 1999 zuwa 2007 ta yi ruwa da tsaki don gyara hanyoyin jin dadin ma’aikata.

Ya kuma bayyana cewa, ya ziyarci kasashen waje na Afrika da dama, ya ga yadda ake rike ma’aikata da muhimmanci sabanin yadda Najeriya a yanzu ta maida ma’aikata saniyar ware.

Ya ce a yanzu haka zai tabbatar da farfado da hanyoyin jin dadin ma’aikata a fadin kasar nan.

Ba ASUU kadai ke kukan rashin samun albashin watanni ba, kishiyarta CONUA ma ta yi barazanar daukar mataki kan gwamnatin Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel