Ana Zaton Wuta a Makera: Cibiyar Habaka Shari’a ta Soki Tikitin Musulmi da Musulmi

Ana Zaton Wuta a Makera: Cibiyar Habaka Shari’a ta Soki Tikitin Musulmi da Musulmi

  • Cibiyar yada shari'ar Musulunci ta nuna adawarta a kan tikitin Musulmi da Musulmi a babban zaben shugaban kasa na 2023
  • Kungiyar Musuluncin ta jaddada koyarwar addinin Islama da ke nuni ga yin adalci ga kowa
  • Ta bukaci yan Najeriya da su mutunta kimar manyan addinan kasar tare da yin watsi da duk takarar da aka gina sa kan tushen addini

Cibiyar habaka Shari'a ta yi watsi da tikitin Musulmi da Musulmi daga bangaren kowace jam'iyyar siyasa, tana mai kira ga yan Najeriya da su duba kimar manyan addinai a Najeriya, Leadesrhip ta rahoto

Da yake jawabi a wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na al'ummar Musulmi a arewacin Najeriya, shugaban cibiyar habaka Shari'a na kasa, Aminu Inuwa Muhammad, ya bayyana cewa sun jajirce wajen tabbatar da akidar Musulunci na gaskiya da adalci.

Kara karanta wannan

Emefiele Yana Amfani Da Matsayinsa Don 'Azabtar' Da Yan Siyasa, Gwamnan Arewa Mai Karfin Fada Aji Ya Yi Zargi

Shettima da Tinubu
Zaben 2023: Cibiyar Habaka Shari’a Ta Yi Watsi Da Tikitin Musulmi Da Musulmi Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Muhammad ya kuma bukaci yan Najeriya da su bijirewa kwadayin yin zabe da aka gina shi bisa tushen addini.

Leadership ta nakalto Muhammad yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Yana da mahimmanci a bukaci dukkanin yan takarar shugaban kasa su sadaukar da kansu wajen cika muradin yan Najeriya ta hanyar tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan, don haka su tabbatar da ci gaba da hadin kan al'ummar kasar.
"Cibiyar habaka Sahari'a ta jajirce kan akidar Musulunci na gaskiya da adalci ga kowa. Don haka tana bukatar dukkanin yan Najeriya da su sake tabbatar da jajircewarsu na kimanta manyan addinan Najeriya da yin watsi da duk wani tikitin takarar shugabancin kasa da aka yi sa kan tushen addini.
"Tun dawowar mulkin damokradiyya a 1999, duk da shakkun da wani bangare na kasashen duniya ke yi, Najeriya ta ci gaba da mika mulki cikin lumana musamman a 2007 da 2015.

Kara karanta wannan

Shugabancin Kasa Na 2023: A Karshe Jonathan Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC

"Yan Najeriya sun nuna jajircewarsu a damokradiyya. Ana ta fuskantar manyan barazana ga wanzuwar Najeriya tun mulkin mallaka na farko, yakin basasa da kuma ayyukan yan aware na baya-bayan nan. Duk da munanan hasashe daga kungiyar kasar waje, Najeriya ta rayu.
"Kamar yadda aka saba mika mulki a baya, yan siyasa sun zafafa siyasa a shirye-shiryem zabukan 2023. Saboda haka Cibiyar habaka Shari'a ta yanke shawarar zaman tattaunawa don magance wadannan matsaloli da suka kasance masu muhimmanci ga rayuwa da zaman lafiyar kasar, musamman kasancewar sun shafi makomar Musulunci da Musulmai a Najeriya."

Zan yi muhawara daga safe har dare, Tinubu

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin yin muhawara daga safe har dare.

Tinubu ya bayyana hakan ne a birnin Landan yayin da yake martani ga masu sukarsa cewa baya son fafatawa da sauran abokan hamayyarsa a zaben shugaban kasa na 2023.,

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng