Matar Fitaccen Dan Takarar Gwamna Da Aka Tura Gidan Yari Na Shekaru 42 Ta Yi Masa Kamfe

Matar Fitaccen Dan Takarar Gwamna Da Aka Tura Gidan Yari Na Shekaru 42 Ta Yi Masa Kamfe

  • Mata da magoya bayan Sanata Albert Bassey Akpan, dan takarar gwamna na YPP, sun yi masa gangami a ranar Juma'a, 9 ga watan Disamba a karamar hukumar Etim Ekpo a jihar Akwa Ibom
  • Babban kotun tarayya da ke Uyo ne yanke wa Sanata Akpan daurin shekaru 42 a gidan yari a ranar Alhamis
  • Amma, matarsa, abokin takararsa da wasu magoya bayansa ba su dena masa kamfe ba

Akwa Ibom - Duk da cewa yana gidan yari, matar Sanata Albert Bassey Akpan, dan takarar gwamna na jam'iyyar Young Peoples Party, YPP, a jihar Akwa Ibom, sun fara kamfe a madadinsa.

The Cable ta rahoto cewa an yi kamfen din Akpan ne a ranar Juma'a, 9 ga watan Disamba a karamar hukumar Ekpo karkashin jagorancin abokin takararsa, Asuquo Amba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bakin Ciki, Hawaye Sun Kwaranya Yayin Da Shahararren Malamin Addini Ya Kwanta Dama A Najeriya

YPP kamfe
Matar Fitaccen Dan Takarar Gwamna Da Aka Tura Gidan Yari Ta Yi Masa Kamfe. Hoto: YPP Akwa Ibom state.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa daruruwan mutane ne suka halarci gangamin don nuna goyon bayansu ga sanatan da aka daure.

Akwa Ibom 2023: Matar Akpan ta yi magana

Da ta ke jawabi ga magoya bayansa a wurin taron, Imabong ta ce babu gidan yarin da ke da girmar da zai iya dakatar da 'abin da mutane ke so.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce:

"Sanata Bassey Albert -OBA har yanzu yana takarar, Zai ni nasara ba zai karaya ba. Babu gidan yarin da ya isa ya dakatar da abin da mutane ke so."

Shugaban kwamitin kamfe ya yi magana

A bangarensa, Emem Akpabio, shugaban kwamitin kamfen din, ya ce daure Sanata Akpan da aka yi 'wani tsaiko ne na dan lokaci da aka yi don gwada imaninsu kuma a daukaka YPP zuwa matakin yanci.'

Ya kwatanta daure sanatan da tsohon shugaban kasa Nelson Mandela da Annabi Yusuf a Bible.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

Nyeneime Andy, shugaban jam'iyyar YPP a jihar, ya ce jam'iyyar ta kara karfi a Akwa Ibom.

Isa Ashiru Ya Bayyana Shirinsa Na Karbe Mulki A Hannun APC a Kaduna

Dan takarar gwamna na jihar Kaduna a karkashin jam'iyyar PDP, Isa Ashiru ya yi alkawarin canja tsarin makarantun gwamnatin jihar idan ya zama gwamna a 2023.

Radio Nigeria ta rahoto cewa Ashiru ya yi wannan alkawarin ne yayin taro da ya yi da mambobin kungiyar yan jaridar kasa reshen jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164