Kotu Ta Kori Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Ebonyi Daga Takara a 2023
- Babbar Kotun tarayya ta soke tikitin takarar shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ebonyi a zaben 2023
- Haka zalika Kotun ta ayyana Barsita Igboke a matsayin halastaccen ɗan takarar majalisar jiha na mazaɓar Ezza ta arewa maso yamma a APC
- Da yake martani, Barista Igboke yace wasa ya ƙare, kotu ta tabbatar da nasarar demokardiyya
Ebonyi - Babbar Kotun tarayya mai zama a Abakaliki, ta kori shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Ebonyi, Hon. Victor Chukwu, daga matsayin ɗan takarar APC a mazaɓar Ezza ta arewa maso yamma
Ɗan majalisar ya kasance mamban jam'iyyar PDP kafin daga bisani ya sauya sheƙa zuwa APC tare da gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Chukwu ya rasa takararsa ne sakamakon taƙaddamar da ta biyo bayan zaɓen fidda gwani da kuma rashin sahihancin zama cikakken mamban APC a jihar.
Da yake yanke hukuncin Alƙalin Kotun mai shari'a Riman Fatum, yace idan aka yi la'akari da hukuncin alkalin babbar Kotun jiha, Chukwu ya zama cikakken mamban APC a 24 ga watan Mayu, 2022 bayan an rufe sayar da Fom ɗin takara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma ƙara da yanke cewa Barista Leonard Nweke Igboke shi ne ya cancanta kuma ya zama halastaccen ɗan takarar majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Ezza ta arewa maso yamma a inuwar APC.
Kotun ta umarci hukumar zaɓe INEC ta goge sunan Honorabul Chukwu daga shafinta na yanar gizo kana ta sauya shi da Leonard Nweke Igboke a matsayin halastaccen ɗan takarar APC a 2023.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa wannan hukuncin ya kawo ƙarshen rigingimun da suka biyo baya kan sahihin ɗan takarar APC na mazaɓar Ezza ta arewa maso yamma a zaɓen 2023.
Martanin wanda Kotu ta tabbatarwa takara
Da yake tsokaci kan hukuncin, Barista Igboke yace matakin da Kotu ta ɗauka nasara ce mai girma ga Demokaraɗiyya. A cewarsa:
"Na ji daɗi godiya ga Allah wanda ya dawo mun da fatana da kuma burin mutanen mazaɓa ta. Hukuncin ya ƙara tabbatar da cewa Shari'a ce gatan na ƙarshe ga kowa."
"Ina tabbatar wa mutane cewa idan na zama ɗan majalisarsu zasu samu wakilci mai kyau, wasan ya ƙare, Demokaraɗiyya ta yi nasara."
A wani labarin kuma Babbar Kotun tarayya ta Abuja ta soke tikitin baki ɗaya 'yan takarar jam'iyyar PDP a Jihar Ebonyi
Mai shari'a Binta Nyako, yayin da take yanke hukuncin ranar Talata tace PDP ta saɓa wa hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara kan sahihin shugaban jam'iyyar na jiha, ta gudanar da zaben karkashin wani daban.
Sai dai Mai shari'a Nyako ta baiwa babbar jam'iyyar hamayya ta ƙasa wa'adin kwanaki 14 ta shirya sabon zaben fidda gwani ko ta rasa 'yan takara a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng