Uwargidar Bola Tinubu Ta Fadi Wadanda Mai Gidanta Zai Ba Muhimmanci a Gwamnatinsa
- Oluremi Tinubu tace idan mulki ya fada hannun Bola Tinubu, za a ba mata da matasa muhimmanci
- Sanatar tace daga cikin inda gwamnatin APC za ta fi ba karfi, akwai bangaren karfawa matasa da mata
- Mai dakin ‘dan takaran shugaban kasa tayi wannan alkawari a wajen taron da suka yi a jihar Legas
Lagos - Matar ‘dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC Sanata Oluremi Tinubu tayi wa mutanen Legas ta tsakiya godiya na goyon bayanta.
Leadership tace Oluremi Tinubu ta godewa mutanenta bayan sun taimaka mata wajen kafa tarihin zama macen farko da ta je majalisar dattawa sau uku.
Sanatar tayi jawabi ga mata da ke goyon bayan jam’iyyar APC daga jihohin Kudu maso yammacin Najeriya a taron kamfe a filin wasan Mobolaji Johnson.
A jawabinta, jaridar tace Tinubu ta yabi Mai dakin abokin takarar mijinta, Hajiya Nana Shettima, tace mata ce da ta damu da halin da mutanenta ke ciki.
Haduwarmu da Nana Shettima - Tinubu
Sanatar take cewa ta fara haduwa da Hajiya Nana Shettima ne a lokacin da ita take jagorantar kwamitin harkokin mata a majalisar dattawan Najeriya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Remi Tinubu tace bincike ya kai su sansanin ‘yan gudun hijira da ke jihar Borno, a lokacin mai gidan Nana Shettima yana kan kujerar gwamnan jihar.
Tsohuwar uwargidar ta jihar Legas tace tun a wancan lokaci ta fahimci yadda Nana Shettima ta damu da halin da mutanenta ke ciki, tana taimakawa IDP.
Tinubu zai yi da mata da matasa
A nan ne uwargidar ‘dan takaran shugaban kasar tace idan har aka yi dace jam’iyyar APC ta lashe babban zabe, Gwamnatin Tinubu za ta taimakawa mata.
Ba ga mata kadai Tinubu zai tsaya ba, mai dakinsa tace zai maida hankali sosai wajen ganin an kula da duk abin da ya shafi ba matasa aiki a Najeriya.
"Zan iya tabbatar maku da cewa harkokin mata da nemawa matasa ayyukan yi su ne za su zama gaba a mulkin Tinubu/Shettima."
- Remi Tinubu
Mata sun halarci gangamin APC
Dr. Ibijoke Sanwoolu ta karbi masaukin irinsu Noimot Salako-Oyedele; Bamidele Abiodun, Linda Ayade Dr. Zainab Shinkafi-Baugudu da Kafayat Oyetola.
A wajen taron an ga Folasade Tinubu-Ojo, Yetunde Adesanya, Dr. Betta Edu, da Zainab Ibrahim.
An shirya taron ne domin a tallata takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, sannnan aka yi wa mata alkawarin za a rika damawa da su.
‘Yan Najeriya su saurari takarar Kirista-Kirista
An samu labari cewa Sanata Oluremi Tinubu a matsayinta na Fasto tace abin da APC tayi a zaben 2023, ya nuna an kama hanyar ganin tikitin Kiristoci zalla.
Uwargidar ‘dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar APC tace tikitin Tinubu/Shettima ya bude kofar tsaida Kirista-Kirista, abin da ba a saba ba.
Asali: Legit.ng