Shugabancin Kasa Na 2023: A Karshe Jonathan Ya Bayyana Matsayarsa Kan Tikitin Musulmi Da Musulmi Na APC
- Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya yi hasashen abin da tikitin musulmi da musulmi na APC zai iya janyo wa a Najeriya
- Tsohon shugaban kasa ya bayyana damuwarsa cewa tikicin yan takara masu addini daya zai kawo cikas ga wakilcin mabanbantan addini a kasar
- Zabin Sanata Kashim Shettima da Bola Ahmed Tinubu ya yi a matsayin abokin takararsa ya sa shugabannin kiristoci da dama sun juya masa baya
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya ce tikitin musulmi da musulmi da jam'iyyar APC ta yi zai kawo koma baya ga wakilcin mabanbantan addini a kasar.
Jonathan a hirar da aka yi da shi a wani littafi da aka wallafa mai suna 'My Time As Chaplain In Aso Rock,' da aka gabatarwa al'umma a ranar Talata, 6 ga watan Disamba, The Punch ta rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Na damu kan batun tikitin musulmi da musulmi ko kirista da kirista, in ji Jonathan
Ya ce:
"Da na zama mataimakin shugaban kasa, al'adar shine ian shugaban kasa kirista ne, mataimakin sa zai kasance musulmi da kishiyar hakan.
"Muna da bukukuwar addinai a Najeriya, kuma, ranar kasa, kuma akwai sallah Juma'a da addu'ar kiristoci.
"Yan Najeriya masu addini ne, shi yasa na ke damuwa kan batun tikitin musulmi da musulmi da kirista da kirista. Eh, Musulmi da musulmi da Kirista da Kirista za su iya mulkar jiha. Amma, ina tambaya, 'wane zai wakilci dayan bangaren idan mun zo yin bukukuwar kasa?."
Tun bayan gabatar da Shettima a matsayin abokin takara, dan takarar shugaban kasar na APC ya ta yin kokarin gamsar da kiristoci a kasar cewa ba saboda addini ya yi zabin ba.
Kukah: Matsalar Najeriya ba tikitin musulmi da musulmi bane, Nagartattun shugabanni ake so
Bishop din katolika na Sokoto, Mathew Kukah ya ce ba mai ceto Najeriya ta ke bukata ba a shekarar 2023, abin da ta ke bukata shine wanda zai daidaita kasar kan alkibla, ba tare da la'akari da harshe ko addini ba.
Kukah ya ce ba za su so su sake yin kuskure ba na dora dukkan burinsu kan wani mutum guda da za su zaci zai cece su, kamar yadda Arise TV ta rahoto.
Asali: Legit.ng