Bola Tinubu Ya Tsokano INEC, Hukumar Zabe Tayi Masa Kaca-Kaca kan Shirin 2023

Bola Tinubu Ya Tsokano INEC, Hukumar Zabe Tayi Masa Kaca-Kaca kan Shirin 2023

  • Hukumar zabe na kasa, INEC tayi raddi biyo bayan wasu kalamai da aka ji daga bakin Bola Tinubu
  • Tinubu yana da shakku a kan yadda za ayi amfani da BVAS a zaben da INEC za ta shirya a 2023
  • Wani babban Hadimin shugaban hukumar INEC yace an shirya zabuka a baya da na’urar zamanin

Abuja - Hukumar zabe na kasa watau INEC ta ragargaji Asiwaju Bola Tinubu a dalilin shakkun da ya nuna a kan amfani da na’urorin zamani a zaben 2023.

Da ya je Landan, an ji ‘Dan takaran yana cewa INEC ba ta bada tabbacin cewa za ta iya yin amfani da BVAS da kafar ganin sakamakon zabe kai-tsaye ba.

Punch tace an samu wani jami’in hukumar zabe na kasa da ya maida martani ga Bola Tinubu, yace sun dade suna bayanin na’urorin da za ayi aiki da su.

Kara karanta wannan

Kasar Birtaniya Tayi Magana a Kan ‘Dan Takaran Shugaban Kasa da Za Ta Goyi Baya

Hukumar tayi mamakin jin matsayar ‘dan takaran shugaban kasar na APC a lokacin da an yi amfani da na’urar wajen shirya zabe a Ekiti, Osun da Anambra.

Martanin Rotimi Oyekanmi

Rotimi Oyekanmi yace tun shekarar 2020, hukumar INEC take yi wa al’umma karin haske a game da siffofi, amfani da kuma muhimmancin na’urorin BVAS.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jaridar tace Oyekanmi shi ne babban sakataren yada labarai na shugaban hukumar INEC.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a Chatham house Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

INEC tayi wa jam'iyyu bayani a kan BVAS

"Tun a 2020, INEC take magana a kan BVAS mai tantance masu zabe, siffofinsa, aikinsa da amfaninsa lokacin da ya maye gurbin na’urar tantance katin zabe.
A duk zaben bayan wata uku da hukumar zabe na kasa take yi da jam’iyyun siyasa, ana gabatar da BVAS, an yi taro fiye da sau biyar, koyaushe ana magana a kai.

Kara karanta wannan

Siyasa Ba Hauka ba ce, Peter Obi ya Fadi Dalilinsa na Mutunta ‘Dan takaran PDP, Atiku

Tunani na shi ne shugabanni da sakatarorin duk jam’iyyun siyasan masu halartar taronmu, sun yi wa ‘yan takararsu na shugaban kasa bayanin abin da aka tattauna.
Bugu da kari kuma, mun yi zaben gwamnoni a jihohin Ekiti, Osun da Anambra duk da BVAS, kuma kowa ya gamsu cewa an yi adalci da gaskiya a zabukan nan.
Gwamnonin nan suna cin moriyar kujerunsu hankali kwance a yau. Kuma ka da a manta, an yi amfani da shi (BVAS) wajen zaben kananan hukumomi a Abuja."

Birtaniya ba ta da 'Dan takara a Najeriya

Rahoto ya zo cewa Jakadar kasar Birtaniya ta hadu da Shugaban Jam’iyyar APC a Sakatariyarsu a Abuja, ta ja kunne a kan murde zaben da za ayi a 2023.

A wajen Catriona Laing da kasar Ingila, babu wani bambanci tsakanin Bola Tinubu, Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso na APC, PDP, LP da NNPP.

Kara karanta wannan

Atiku ne ya Lashe Zaben 2019, Fashi Aka yi Masa, Titi Atiku ta Fasa Kwai

Asali: Legit.ng

Online view pixel