2023: Ba Zasu Iya Tsinana Komai Ba, Gwamna Sule Ya Caccaki Yan Adawa

2023: Ba Zasu Iya Tsinana Komai Ba, Gwamna Sule Ya Caccaki Yan Adawa

  • Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa yace jam'iyyun adawa ba su kai matakin da zasu iya ɗauke masa hankali ba
  • Sule na ɗaya daga cikin gwamnonin jam'iyyar APC a shiyyar arewa dake kokarin ganin sun zarce zangon mulki na biyu a zaɓen 2023
  • Wani jigon APC a Lafiya, babban birnin Nasarawa yace har yanzun PDP ba ta yi kwarin sake komawa kan madafun iko ba

Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, yace damuwarsa shi ne ya lalubo hanyar haɓaka jiharsa da inganta rayuwar talakawa amma ba 'yan adawa ba musamman PDP.

Jaridar Vanguard tace gwamna Sule ya faɗi haka ne yayin ci gaba da yawon tallata kudirinsa na neman tazarce wanda ya gudana a ƙaramar hukumar Doma.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.
2023: Ba Zasu Iya Tsinana Komai Ba, Gwamna Sule Ya Caccaki Yan Adawa Hoto: vanguardngr
Asali: Facebook

Yace 'yan adawa na kokarin kawar da tunaninsa yayin da ya maida hankali wajen samar da duk wani abu da zai kawo wa jihar Nasarawa cigaba.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Jihar Arewa Ya Tiƙa Rawa Bayan Magoya Bayansa Sun Mutu a Hatsari

A kalaman gwamna Sule yace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na ƙi yarda na raba hankalina a kokarin ganin mutane sun samu ingantacciyar rayuwa. Ba zan fara shiga rudani ba saboda yan rayukar ƙarya watau tsagin masu adawa, waɗanda babu abinda zasu iya tsinanawa."

Bayan haka, Gwamnan ya roki mazauna yankin ƙaramar hukumar Doma su ci gaba zaman lafiya da kuma goyon bayan jam'iyyar APC da gwamnatinsa a fafutukarta na sauya jihar.

PDP ba zata iya dawowa kan mulki ba - Jigon APC

Haka nan, wani babban jigon APC a Lafiya, Alhaji Reyyanu Iliyasu, ya yi fatali da raɗe-raɗin cewa PDP ta farfaɗo da karfinta, zata kwace mulkin Nasarawa da ya subuce mata a 2011.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba, jigon jam'iyyar mai mulki yace PDP ba ta da wani muhimmin aikin raya ƙasa da ta bari wanda zata iya jawo hankalin mutane su zaɓe ta.

Kara karanta wannan

Wa Zaka Zaba Tsakanin Atiku da Peter Obi Idan Baka Cikin 'Yan Takara? Tinubu Ya Ba Da Amsa Mai Jan Hankali

Bugu da ƙari, yace baki ɗaya shekarun da jam'iyyar PDP ta kwashe tana mulki sun tafi a banza a wofi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

An Tona Asirin Fitaccen Ɗan Takarar Shugaban Kasa, An Gano Atiku Yake Wa Aiki

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban kasa na SDP ya yi ikirarin cewa jam'iyyar Peter Obi reshe ne kawai na PDP

Da yake bayyana yunkurin jam'iyyarsa na kulla ƙawance da LP, Ademola Adebayo, yace da LP da PDP duk abu ɗaya ne amma da farko SDP ta nemi yin maja da LP.

Jam'iyyar LP da ɗan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, na cikin jerin mutum uku da ake kallon ɗayansu ne zai gaji shugaban ƙasa Buhari a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262