Ba Zan Abi Atiku Ko Peter Obi Ba Idan Bana Cikin 'Yan Takara, Tinubu

Ba Zan Abi Atiku Ko Peter Obi Ba Idan Bana Cikin 'Yan Takara, Tinubu

  • Mai neman kujera lamba ɗaya a Najeriya a zaɓen 2023, Bola Tinubu, yace ba zai iya zaben Atiku ko Peter Obi ba
  • Tsohon gwamnan jihar Legas yace dukkaninsu ba su cancanci zama shugaban ƙasa ba kuma ba su kama kafarsa ba
  • Yanzu haka Tinubu na Landan na ƙasar Birtaniya inda ya yi jawabi a Chatham House kana ya yi hira da BBC

Ɗan takarar shugaban ƙasa karkashin inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, yace ba zai zabi ko ɗaya daga cikin abokan hamayyarsa ba idan da ba ya cikin 'yan takara a 2023.

Channels tv ta rahoto cewa Tinubu ya fayyace a fili cewa ba zai zaɓi Peter Obi na jam'iyyar LP ko Atiku Abubakar na PDP ba ko da kuwa a ce ba ya cikin masu neman gaje Buhari.

Kara karanta wannan

A Karshe ‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Yi wa Duniya Bayanin Yadda Ya Mallaki Dukiyarsa

Manyan 'yan takara uku na sahun gaba.
Ba Zan Abi Atiku Ko Peter Obi Ba Idan Bana Cikin 'Yan Takara, Tinubu Hoto: channelstv
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Legas ya faɗi haka ne a wata hira da kafar BBC News ranar Litinin jim kaɗan bayan jawabi a Chatham House, Landan na ƙasar Birtaniya.

Yayin da aka tambaye shi wanda zai kaɗa wa kuri'arsa tsakanin Atiku da Peter Obi idan ba ya cikin masu neman takara, Tinubu yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ko ɗaya daga cikinsu ba zan zaɓa ba saboda ba su cancanta ba kamar saura, ba su da wani tarihi, duk cikinsu babu wanda ya cancanta sai ni kaɗai."

Mahassada ke sukar hanyar tara dukiyata - Tinubu

Ɗan takarar shugaban ƙasan ya ƙara da cewa hassada ce ke ingiza wasu na sukar dukiyar da Allah ya ba shi. Yace ya tara dukiya ne ta hanyar zuba hannayen jari.

A ruwayar Vanguard, Tinubu ya ce:

"Bana musu kan dukiya ta, ni aka fi sanya wa ido, ni ne gwamnan da aka fi suka a tsagin adawa tsawon shekara Takwas kuma tun da na bar Ofis ban sake karɓan mukamin gwamnati ba. Ban karɓi kwangila ba."

Kara karanta wannan

"Ka Biyo Ni": Wata Dirarriyar Budurwa Ta Nemi Ɗan Acaba Ya Kwanta da Ita, Bidiyon Ya Girgiza Mutane

Jerin Sunayen Jihohin Arewa 6 da Fafatawa Zata Yi Ɗumi Tsakanin Atiku da Tinubu Tare da Dalilai

A wani labarin kuma mun tattara muku sunayen wasu jihohin arewacin Najeriya 6 da gwabaza wa zata yi zafi tsakanin APC da PDP

Yankin arewa maso gabas shiyya ce da yanzu haka take da ɗan takarar shugaban ƙasa watau Atiku Abubakar da ɗan takarar mataimaki, Sanata Kashim Shettima.

Idan har ɗaya daga cikin manyan jam'iyyu APC ko PDP ta lashe zaben shugaban kasa a 2023, shiyyar zata samu ko dai mutum lamba ɗaya ko lamba na biyu a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel