2023: Sanatan APC A Shahararriyar Jihar Arewa Ya Magantu Kan Sauya Sheka Zuwa PDP
- Sanatan mai wakiltar mazabar Niger East, Sani Musa, ya yi martani kan rahoton cewa yana shirin fita daga APC ya koma PDP
- Sanata Musa ya ce babu kanshin gaskiya a rahoton da ya ce yan siyasa masu son kulla makirci ne suka kirkira, kuma ya bukaci al'umma su yi watsi da rahoton
- Jigon na jam'iyyar APC ya ce kan yan takarar APC a Neja a hade ya ke kuma abin da ke gabansu shine aiki kan yadda za su ci zabe a 2023
Jihar Neja - Sanata Sani Musa mai wakiltar Niger East a karkashin jam'iyyar APC ya ce ba shi da niyyar sauya sheka zuwa wata jam'iyyar duk da jita-jita da ake yada wa.
Ya bayyana hakan cikin sanarwa da ya fitar a Minna a ranar Alhamis kan rahotonni da suka fito na cewa yana shirin komawa jam'iyyar PDP, wanda ya ce aikin masu makirci ne, rahoton Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwar mai dauke da sa hannun Alhaji Nma Kolo, mamba na kwamitin shawarwari na kamfen din Sani Musa, sanarwar ta bukaci mutane su yi watsi da rahoton.
Sanarwar ta ce:
"Har yanzu Sanata Sani dan jam'iyyar APC ne jajirtacce da ke aiki dare da rana domin ganin nasarar jam'iyyar a 2023."
Yan siyasa masu son kulla makirci ne suka kirkiri rahoton - Sani
Ya soki wadanda suka wallafa rahoton saboda sun gaza gano ainihin mutanen da ake ikirarin yana shirin sauya sheka.
Sanarwar ta ambato yana cewa:
"Musa, sanata mai ci yanzu na Niger East ba shi da alaka da maganan sauya sheka.
"APC a jihar Neja kanta a hade ya ke kuma yan takarar mu suna aiki tare don nasara a babban zaben da ke tafe ba tare da damuwa ba."
Sanarwar ta kuma bayyana Musa a matsayin dan siyasa mai son cigaba wanda ba zai taba take damar wani dan siyasa na shiga jam'iyyar da ya ke so ba.
A cewar rahoton na Vanguard, ya yi kira ga magoya bayansa su yi watsi da labaran karya da wasu yan siyasa masu son kitsa makirci ke kirkira.
Dandazon yan APC sun sauya sheka zuwa PDP a Sokoto
A wani rahoton, Mallam Sai'idu Umar, dan takarar kujerar gwamna na jam'iyyar PDP a Sokoto, ya tarbi mambobin jam'iyyar APC a kalla 2,343 zuwa cikinsu.
Leadership ta rahoto cewa dubban yan APC sun koma PDP a Mainiyo da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.
Asali: Legit.ng