Kasar Birtaniya Tayi Magana a Kan ‘Dan Takaran Shugaban Kasa da Za Ta Goyi Baya
- Jakadar Birtaniya ta hadu da Sanata Abdullahi Adamu da sauran shugabannin jam’iyyar APC na kasa
- atriona Laing ta shaidawa APC mai mulki cewa burin ta shi ne ayi adalci a zaben shekara mai zuwa
- Laing tace Ingila ba ta da ‘dan takara a zaben badi, za tayi aiki da duk wanda ya zama shugaban kasa
Abua - Gwamnatin Birtaniya ta gargadi jam’iyyar APC cewa kasar Ingila ba ta da wani ‘dan takara da take goyon baya a zaben shugaban Najeriya.
Jaridar Sun ta rahoto Jakadar Ingila a Najeriya, Catriona Laing, tana wannan bayani a yayin da ta jagoranci jami’anta zuwa sakatariyar APC a Abuja.
Catriona Laing ta zauna da Abdullahi Adamu da ‘yan majalisarsa na NWC a ranar Laraba, 7 ga watan Disamba 2022, inda suka tattauna kan zabe.
Laing tace wannan zama da tayi da APC NWC yana cikin jerin zaman da za tayi da masu ruwa da tsaki musamman jam’iyyun siyasa kan shirin 2023.
Ko da an yi zaman ne a bayan labule, bayan an fito, Jakadar ta shaidawa manema labarai cewa tattaunawarsu ta kunshi ba kowa damar kada kuri’a.
The Guardian tace gwamnatin Birtaniya ta ja kunne a kan yi wa masu zabe barazana, tace tana so a gudanar da zabe ba tare da magudi da murdiya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin zuwa Sakatariyar APC
"Wannan yana cikin jerin taron da zan yi da jam’iyyun siyasa, ‘yan takarar kujerar shugaban kasa da kuma shugabannin jam’iyyu.
Yau da shugaban APC zan zauna domin in fada masa sakonmu game da zaben 2023.
Mun kuma tattauna kadan a kan abubuwan da ake bukata wajen zaben nan. Mun yi magana a kan tsaro, a bari ayi zabe babu barazana.
Sannan mun yi magana a kan samun yanayin da ake bukata, a bar mutane masu kada kuri’a su zabi duk ‘dan takaran da suke so.
Ingila da Najeriya na da alaka mai karfi, mu na so Najeriya ta cigaba ta fuskar damukaradiyya, muna so mu bada gudumuwarmu.”
- Catriona Laing
Wanene 'dan takaran Ingila?
An rahoto Laing tana mai cewa Ingila ba ta da wani ‘dan takara da take goyon baya a zaben.
Abin da kasar take so shi ne ayi zabe mai nagarta da adalci, Jakadar tace kasarta za tayi aiki hannu biyu-biyu da duk wanda ya yi nasarar karbar mulki.
Buhari ya je kasashe 40
A wani rahoto da aka fitar, an fahimci daga 2015 zuwa 2022, duk kusan bayan kwana 37, sai jirgin fadar Shugaban kasa ya bar Najeriya zuwa wata kasa.
Muhammadu Buhari ya yi watanni 90 yana rike da mulkin Najeriya, a tsawon wannan lokaci, ya shafe kusan wata 8 yana jinya a birnin Landan
Asali: Legit.ng