Lauya Ya Maka Atiku Abubakar, FG da INEC a Gaban Kotu, Yana So a Hana Atiku Takara
- Dakta Jezie Ekejiuba, wani lauya mai zama a garin Onitsha ta jihar Anambra, ya maka Atiku Abubakar, ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP a gaban kotu
- Ekejiuba bai tsaya nan ba, ya hada da Gwamnatin tarayya tare da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da suka bar Atiku ya tsaya takara
- Lauyan ya bukaci a hana Atiku takara saboda kasancewarsa ‘dan arewacin Najeriya, barinsa takara take hakkin Ekejiuba ne matsayinsa ‘dan kudu
Anambra - Wani lauya mazaunin garin Onitsha dake jihar Anambra, Dakta Jezie Ekejiuba, ya maka Gwamnatin tarayya, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar, a gaban kotu.
Ekejiuba yana son a hana Atiku takarar shugabancin kasa a zaben 2023 dake gabatowa.
Lauyan yace barin Atiku yayi takara zai kawo karantsaye ga hakkinsa a matsayinsa na ‘dan Najeriya.
Ya kara da cewa, zai zama babban kuskure ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ‘dan arewa ya mika mulki hannun Atiku, wani ‘dan arewan a zaben 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lauyan ya jaddada cewa, mulkin karba karba tsakanin arewa da kudu wanda ya fara 1999 dole ne a mutunta shi kuma kowanne ‘dan Najeriya dole ne ya ji cewa shi ‘dan kasa ne.
A karar mai lamba FHC/AWK/CS/198/2022 wacce aka shigar gaban babban kotun tarayya dake Awka, an mika antoni janar na tarayya matsayin wanda ake kara na biyu, INEC ta uku, PDP ta hudu da Atiku na biyar.
Jaridar Punch ta rahoto cewa, Ekejiuba wanda shi ne shugaban kungiyar masu hakkin saka kuri’a na Najeriya, yana bukatar diyyar N200m daga kowanne cikin wadanda ake kara da kuma kudin barna na barazanar take hakkinsa na ‘dan kasa.
Ekejiuba a shari’ance yayin goyon bayan bukatar, ya bayyana cewa hakkinsa na ‘dan kasa ya samu kariya a karkashin sashi na 42 sakin layi na 1 na kundin tsarin mulkin kasar nan da aka gyara.
Lauya ya kai Atiku kotu, Yana so a hana shi takara
A wani labari na daban, wani lauya mai suna Johnmary Jideobi mazaunin Abuja ya kai karar Atiku Abubakar a gaban kuliya.
Lauyan ya sanar da babbar kotun tarayyar cewa Atiku Abubakar ba haifaffen ‘Dan Najeriya bane.
Asali: Legit.ng