Siyasa Ba Hauka ba ce, Peter Obi ya Fadi Dalilinsa na Mutunta ‘Dan takaran PDP, Atiku
- ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasar nan a inuwar Labour Party yace yana ganin girman manyansa
- Wannan ya sa ko me zai faru kuwa, Mr. Peter Obi yace ba zai taba cin mutuncin Alhaji Atiku Abubakar ba
- Obi yace a yankin da ya fito, kowa na girmama manya saboda haka yake ganin girman ‘dan takaran na PDP
Abuja - ‘Dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar hamayya ta LP, Peter Obi, yace bai da niyyar cin mutuncin abokan gabansa a 2023.
Vanguard ta rahoto Peter Obi yana mai cewa ba zai buge da yin gardama ko kiran sauran ‘yan takaran shugaban kasa da sunaye da sunan siyasa ba.
Obi ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya tattauna da masu ruwa da tsaki daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya a wani taro da aka yi a Abuja.
‘Dan siyasar ya yi amfani da wannan dama wajen yin watsi da rade-radin da ake yi na cewa yana yakar ‘dan takaran PDP a 2023, Atiku Abubakar a boye.
Abin da yake gabanmu - Obi
An rahoto ‘Dan takaran takaran yana cewa abin da shi da sauran jagororin jam’iyyar LP a kasar nan suka damu da shi, shi ne ceto mutane daga talauci.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Atiku Abubakar babban yayana ne da nake ganin mutuncinsa har gobe. A inda na fito, kowa yana girmama manyansa.
Ko da Atiku Abububakar zai zage ni a cikin bainar jama’a, to ni ba zan maida masa martani ba domin yana gaba ni.
Idan har zan ci mutuncin manya na idan na samu kudi ko mulki, to ka da Ubangiji ya mallaka mani su tun farko.
Ba abin da Ubangiji yake so kenan ba.
Dole a girmama manya. Ina da manyan ‘yanuwa, dole in girmama su idan ina so a girmama ni idan na kai shekarunsu.
- Peter Obi
Idan Atiku ya zagi Peter Obi, me zai faru?
Ba a nan abin ya kare ba, Nairaland ta rahoto Obi yana cewa zai zo ya yi kamfe a jihar Adamawa, kuma idan aka yi dace Atiku yana nan, zai zo ya gaida shi.
A cewar ‘dan takaran na LP, Ibo sun saba koyon kasuwanci, da zarar mutum ya kware, sai ya matsa ya bude shagonsa, yace haka ya yi a wajen Atiku.
Duk da suna yakin neman mulki a tare, Peter Obi yace siyasa ba rikici da abokan hamayya ba ne, dukkaninsu sun fito harin kuri’un ‘Yan Najeriya ne.
Tsakanin 'Yan Sanda da IPOB
Labari ya zo cewa Jami’an ‘Yan sandan jihar Imo ta bakin Mike Abattam sun ce ba kowa suka kona ofishin hukumar zabe ba illa ‘Yan kungiyar IPOB.
Sai dai 'Yan IPOB da dakarun Eastern Security Network (ESN) sun ce ba suka yi aika-aikar da ‘yan sanda suke zarginsu da aikatawa a Kudancin kasar ba.
Asali: Legit.ng