‘Yan Sanda Sun Gano Wadanda Suka Kona Ofishin INEC, Asirin Masu Danyen Aikin Ya Tonu

‘Yan Sanda Sun Gano Wadanda Suka Kona Ofishin INEC, Asirin Masu Danyen Aikin Ya Tonu

  • Rundunar Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun zargi IPOB da ESN da kai wa ofishin INEC hari a jihar Imo
  • A cewar Kakakin ‘yan sanda na Imo, Mike Abattam, tsagerun suka yi wannan aiki, kuma ana bincike
  • Sakataren yada labarai na IPOB, yace babu hannunsu a harin domin babu ruwansu da harkar zabe

Imo - Jami’an ‘yan sandan Najeriya suna zargin cewa ‘yan kungiyar IPOB ne suke da hannu a kona ofishin hukumar INEC da aka yi a Oru a jihar Imo.

Daily Trust ta rahoto jami’an tsaron suna cewa dakarun ESN masu rike makamai suka kai harin, ‘yan sanda suka hana su yin ta’adin da suka shirya.

Kakakin ‘yan sandan jihar Imo, Mike Abattam ya yi bayani a garin Owerri, yana cewa miyagun sun jefa bama-baman IED zuwa ofisihin hukumar zaben.

Kara karanta wannan

Ogun: Tsaka Tayi Ajalin Rayukan Mutum 6 ‘Yan Gida Daya Bayan Cin Abincin da ta Fada

Kamar yadda Mike Abattam ya shaidawa manema labarai, 'yan sanda sun yi amfani da kwarewarsu, suka aukawa ‘yan bindigan, suka ji masu rauni.

An jefo bam a ofis

Da suka fahimci karyarsu ta kare, ‘yan bindigan na IPOB sun yi kokarin tserewa a mota, nan take 'yan sanda suka bi su domin ganin sun yi ram da su.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yayin da suke yunkurin tserewa ne suka jefa bam a wani dakin taro, hakan ya yi sanadiyyar lalata tagogi da kayan ofis, amma babu wanda ya ji rauni.

‘Yan Sanda
Wani Jami'in 'Dan Sanda Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

An rahoto Abattam yana cewa ana bincike domin a cafke wadanda suka yi wannan danyen aiki, har aka bada lambar wayar jami’an tsaro da za a tuntuba.

Babu ruwanmu - IPOB

Amma ‘yan kungiyar IPOB da ESN sun ce babu hannunsu a harin da aka kai a karamar hukumar Oru ta yamma, suka ce babu abin da ya shafe su da zabe.

Kara karanta wannan

Dakarun Soji Sun Halaka ‘Yan Bindiga 20 a Niger, Sun Yi Nasarar Ceto Wasu Mutum 5

Guardian ta rahoto Sakataren yada labarai na IPOB, Emma Powerful yace kungiyarsu ba ta tada rikici, sai dai tayi umarni a kauracewa harkar zabe idan ta kama.

Emma Powerful yace babu abin da ya hada kungiyar IPOB da Najeriya da zaben 2023 kuma ba su taba cewa wani ya kai wa INEC ko wani hari da sunanta ba.

Kakakin kungiyar yace sharri jami’an tsaro suke yi masu saboda haka ne har yanzu ba a iya kama ko da mutuminsu daya da ke da hannu wajen yin ta’adin ba.

Aminu ya bada hakuri

An ji labari matashin da wasu suke zugawa ya shigar da kara a kan Aisha Muhammadu Buhari da Jami’an tsaro, ya dawo yana mai bada hakuri.

Aminu Adamu yace tun farko bai yi nufin ya batawa matar Shugaban kasa rai ba, yace abin da ya faru da shi ya isa darasi ga kowa, yace za gyara halinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel