Matsala Mai Tsauri Ta Sake Samun Tinubu Yayin Da ’Yan Legas Suka Yi Alkawarin Marawa Atiku Baya
- Adadi mai yawa na jama’ar jihar Legas ne suka bayyana kauna da goyon baya ga dan takarar shugaban kasan jam’iyyar PDP a ranar Litinin
- Mazauna yankin Kudu masom Yamma sun bayyana goyon bayansu ga Atiku gabanin babban zaben 2023 da ke tafe nan kusa
- Wannan nuna kauna da aka yiwa Atiku ya ba da mamaki a kafar Twitter, mutane da dama sun yi martani
Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya sake samun kwarin gwiwa daga mazauna jihar Legas yayin da zaben 2023 ke gabatowa.
Atiku Abubakar ya samu wannan karuwa ne a yankin Kudu maso Yamma yayin wani taron gangamin siyasa da aka gudanar a filin wasa na Teslim Balogun, inda ‘yan jihar suka yi tururuwa don nuna goyon bayansa.
Ganin yadda taro ya yi taro, ga kuma taron masoya a Atiku a Legas, wani hadiminsa, Eta Uso ya yaba da wannan kauna da aka nunawa uban gidansa a jihar abokin hamayyarsa.
Uso ya rubuta a Twitter cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Soyayya mai ban mamaki, Mun gode, Legas.”
Wannan ci gaba da Atiku ya samu dai ba karamin tsaiko bane ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu, domin kuwa jiharsa ce.
Ana kyautata zaton jihar Legas ce jihar da Tinubu ke da kwarin gwiwa a kai, domin ya yi gwamnan Legas tsawon shekaru. Hakazalika ya yi sanata a Legas.
Shi kansa Atiku ya yada hotunan tarbar da ya samu a Legas.
Malamin addini ya ce a bari Allah ya zaba wa Najeriya shugaba na gaba
Duk da nasarar da ‘yan siyasa ke samu, wani malamin addini na cocin Arewacin Najeriya ya ce kowa ya kwatar da hankali ya mika lamarin siyasar kasar ga ubangiji.
Fasto Joshua Mallum ya ce, ‘yan Najeriya su hada kai, musamman kiristoci kana su mika wuya ga Allah gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Ya fadi hakan ne a wani taron da aka gudanar a Abuja, inda yace Najeriya na bukatar shugaban da zai fitar da ita daga kangin wahala.
Ya bayyana cewa, tunda babu wandan yasan shugaban da zai kawo sauyin, kawai a mai lamari ga ubangiji, shi zai kawo sauki.
Ba zan yi muhawara da kowa ba sai da ka’idoji
A wani labarin kuma, dan takara Tinubu ya ce ba zai tattauna da Peter Obi ba sai ya cika wasu ka’idoji guda hudu da ke nuna ya kai.
Tinubu ya bayyana cewa, ba kuma zai halarci wata zama a gidan talabijin ba sai an cika ka’idojin da ya ba Peter Obi.
Ana ci gaba da kai ruwa rana kan batun tattaunawar Tinubu da sauran siyasa a kasar nan.
Asali: Legit.ng