Tinubu Ya Kawo Sharudda 4 Kafin Ya Amince da Yin Muhawara da Peter Obi a AriseTV

Tinubu Ya Kawo Sharudda 4 Kafin Ya Amince da Yin Muhawara da Peter Obi a AriseTV

  • Dan takarar shugaban kasa a APC, Bola Tinubu ya fadi sharuddansa kafin ya amince da wata tattaunawa ko muhawara gabanin zaben 2023
  • Tinubu, ta bakin kakakin kamfen din APC a matakin kasa, Festus Kayemo ya nemi ganin takardun manufofin Peter Obi na jam'iyyar Labour
  • Tinubu ya kuma bukaci Peter Obi ya lissafo dukkan nasarorin da ya cimma a lokacin da yake gwamnan Anambra tare da bayyana wasu abubuwa guda biyu

Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana kadan daga sharuddansa na yin muhawara da dan takarar shugaban kasan jam'iyyar Labour, Peter Obi.

Sharuddan na Tinubu su ne kuma sharin da ya gindaya kafin ya amince ya bayyana a gidan talabijin da sunan tattaunawa kan manufofinsa na takarar shugaban kasa, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Subut da baka: Tinubu ya sake yin wata katobarar da ta fi ta baya, 'yan Najeriya sun girgiza

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana hakan ne ta bakin kakakin kamfen na shugaban kasa na jam'iyyar APC, Festus Kayemo a ranar Talata 29 ga watan Nuwamba.

Ba zan yi muhawara da Peter Obi ba sai ya cika sharudda 4
Tinubu Ya Kawo Sharudda 4 Kafin Ya Amince da Yin Muhawara da Peter Obi a AriseTV | Hoto: headtopics.com
Asali: UGC

Shin Tinubu zai halarci taron muhawara gabanin zaben 2023?

Ga dai abin da Tinubu ya lissafa game da hakan a matsayin sharudda:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  • Tinubu zai halarci zaman muhawara da Peter Obi ne kadai idan dan takarar na Labour ya nuna manufofinsa na tsayawa takara ga 'yan Najeriya
  • Ya bukaci Peter Obi ya bayyana nasarorin da ya cimma a jihar Anambra a lokacin da yake gwamna kafin halartar wannan muhawara
  • Ya kuma bukaci Peter Obi ya fadi jam'iyyar siyasar da ya kirkira a matsayinsa na jagoran siyasa a kasar nan
  • Hakazalika, Tinubu ya bukaci Peter Obi ya fadi su waye iyayen gidansa na siyasa da masu daura shi a turba kuma ya sanar da 'yan Najeriya ko har yanzu yana tare da wadannan iyayen gidan nasa

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Idan Na Hau Kujerar Mulki Matasa Za Su Sha Romon Dadi, Atiku Abubakar

Idan baku manta ba, a baya Tinubu ya ce ba zai halarci zaman muhawara ko kuma tattauna manufofinsa ga jama'a ba da gidan talabijin na Arise ta shirya.

Jam'iyyun adawa sun sha nuna bukatar yin muhawara da Tinubu kan manufofinsa na takarar badi, amma ya sha nuna hakan ba zai yiwu ba, kamar yadda Vanguard ta ruwairo.

An kirkiri manhajar ba Tinubu tallafin kamfen

A wani labarin kuma, kun ji cewa, wata manhaja ta fito domin tattara kudade da sunan tallafi ga dan takarar shugaban APC, Tinubu.

Wannan manhaja dai za ta karbi kudi ne domin yin kamfen din APC a fadin kasar nan, kamar yadda bayanai suka nuna.

A 2015 APC ta taba karbar kudaden 'yan Najeriya domin yiwa Buhari kamfen din takarar shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel