Abubuwan da Atiku, Obi, Kwankwaso Suka Fada a Taron 'Yan Takaran 2023

Abubuwan da Atiku, Obi, Kwankwaso Suka Fada a Taron 'Yan Takaran 2023

  • Manyan masu harin kujerar shugaban kasa a 2023 sun yi zama na musamman a garin Legas
  • Gidan talabijin Arise TV ya shirya taron domin jin ta bakin wadanda ke neman mulkin Najeriya
  • Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun halarta, Bola Tinubu bai iya zuwa ba

Legit.ng Hausa ta bibiyi tattaunawar da aka yi da manyan masu neman shugabancin Najeriya a 2023, ta rahoto wasu daga cikin abin da suka fada:

Punch tace tattaunar da aka yi ranar Lahadi ta shafi batutuwan ilmi, kiwon lafiya da talauci.

Atiku Abubakar ya bukaci gwamnatin tarayya ta zauna da masu ruwa da tsaki domin ganin yadda za a kawo karshen matsalar yajin-aikin kungiyar ASUU.

A kan wannan batu, Rabiu Kwankwaso yana ganin babu gaskiya daga bangarorin, yace idan ya samu mulki, ba zai yi wasa da hakkokin ma’aikatan jami’a ba.

Kara karanta wannan

Nagode Mama: Aminu Adamu ya Bada Hakuri a Fili, Yayi Alkwari Zai Gyara Halinsa

Shi ma Peter Obi yana ganin abin da ake kashewa a kan harkar ilmi ya yi kadan, sannan ya bukaci a zauna da ASUU domin a samu mafitar da za ta daure.

Yaran da ba su zuwa makaranta

A bangaren yaran da ba su zuwa makarantar boko a Arewacin Najeriya, Atiku Abubakar yace dole a maida hankali a kan lamarin, a ware kudi masu yawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku da Kwankwaso
Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Peter Obi yace a shekaru shida da suka wuce, abin da ake warewa harkar ilmi bai kai 10% ba, yace gwamnatinsa za ta narka kudi domin ganin an samu ilmi.

Shi ma Kwankwaso ya yarda da su, har ya yabi Atiku Abubakar da ya kafa jami’a, amma yace ya kamata a rage kudinta saboda yaran talakawa su iya zuwa.

Ya za a gyara sha'anin kiwon lafiya?

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Dole a zauna da ‘yan kasuwa, a nemi su narka kudinsu a harkar lafiya idan ana so a ga cigaba a Najeriya, wannan shi ne ra’ayin Atiku Abubakar na PDP.

'Dan takaran yana ganin ya zama wajibi gwamnati ta rage facaka ta kuma cire tallafi.

A nan ma Obi yace N2.5tr da aka batar a kan kiwon lafiyar mutum fiye da miliyan 200 ya yi kadan, ya kuma ce akwai karancin makarantun koyon aikin jinya.

Kwankwaso ya bugi kirji yana cewa yana da cikakken koshin lafiya, kuma a asibitocin gida ake duba shi, yace ko da ya samu mulki ba zai fita zuwa ketare ba.

Ba zan zauna a gida ba - Atiku

An samu labari tsohon mataimakin shugaban kasar yana ganin an bar Najeriya a baya, don haka ba zai bari ya kwanta jinya ba sai asibitin kasashen waje.

Yayin da Alhaji Atiku Abubakar yake tsoron asibitocin kasar nan, abokan hamayyarsa, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun ce a gida ake duba lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng