Tinubu Da Atiku Basu Da Isasshen Lokacin Gamawa Da Kudaden Da Suka Tara – Baba-Ahmed

Tinubu Da Atiku Basu Da Isasshen Lokacin Gamawa Da Kudaden Da Suka Tara – Baba-Ahmed

  • Abokin takarar shugaban kasan Peter Obi, Datti Baba-Ahmad ya ce Tinubu da Atiku na bata abokin takararsa
  • Datti ya ce Tinubu da Atiku sun tara kudaden da za su iya kashewa ba a rayuwarsu
  • Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da musayar kalamai yayin da ake ci gaba da tunkarar zaben 2023

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu; da takwaransa na PDP, Atiku Abubakar, basu da isasshen lokacin kashe kudaden da suka tara.

Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a shirin Sunday Politics na Channels TV a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba.

Atiku da Tinubu
Tinubu Da Atiku Basu Da Isasshen Lokacin Gamawa Da Kudaden Da Suka Tara – Baba-Ahmed Hoto: Atiku Abubakar/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Atiku mai shekaru 76 da Bola Tinubu mai shekaru 70 sune kan gaba a takarar shugaban kasa na 2023 daga manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu.

Kara karanta wannan

Abokin Takarar Peter Obi Ya Fasa Kwai, Ya ce Buhari Bai Damu Da Takarar Bola Tinubu Ba

APC da PDP kudi suka iya rabawa amma basu iya shugabanci mai kyau ba

A cewar abokin takarar Peter Obi, jam'iyyun APC da PDP suna da tsari na raba kudade amma ba wai na gudanar da shugabanci nagari wanda zai gyara rayukan al'ummar kasar ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Baba-Ahmed ya ce:

"Babu abu mai kama da wannan a matsayin tsari; batu ne na mutane da ke son karbar kudaden da suka tara. Dole wani ya karbi wadannan kudaden; ba zai yiwu ku barsu su tafi da wannan kudin ba.
"Tinubu bai da isasshen lokaci a rayuwarsa da zai gama kashe wadannan kudaden. Atiku bai da isasshen lokaci a rayuwarsa da zai gama kashe duk wadannan kudaden.
Don haka suna bukatar kashe shi a zaben 2023. Kuma mutane, idan kana da kudaden kashewa, za su karbe abin su."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Abokin Takarar Peter Obi Ya Yi Garumin Zargi A Kan Tinubu

Ya jaddada cewar LP na da kaya amma ba za ta kashe kudaden da ba za ta iya bayar da bayani a kansu ba.

Ya kara da cewar manyan jam'iyyun siyasar kasar biyu suna da abun da ake kira tsari ba tare da shugabanci ba kasancewar sun yi mulkin kama karya a Najeriya tun 1999 lokacin da kasar ta samu yancin kai.

"Jam'iyya daya ce take da tsari na gaskiya, kuma ita ce Labour Party."

Tun 1999 PDP ta samar da shugabannin kaaa uku, Olusegun Obasanjo, Umaru Yar'adua da Goodluck Jonathan wadanda suka yi shekari 16 kafin gwamnatin APC na shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya karbi mulki a 2015.

Buhari bai damu da takarar Bola Tinubu ba, Inji Datti Baba-Ahmed

A gefe guda, mun ji a baya cewa Datti Baba-Ahmed ya ce duk da rawar ganin da Bola Tinubu ya taka wajen ganin ya yi nasara a 2015, shugaban kasa Muhammadu Buhari bai damu da takarar tsohon gwamnan na jihar Lagas ba.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Samu Karɓuwa Har Wurin Mayu Da Masu Sihiri, In Ji Dino Melaye

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng