Olusegun Obasanjo Ya Nuna Inda Ya Dosa, Bai Goyon Bayan Atiku da Kwankwaso
- ‘Yan kungiyar Mzough U Tiv na kabilar Tiv daga Benuwai, sun ziyarci Olusegun Obasanjo a Abeokuta
- Shugaban Mzough U Tiv, Iorbee Ihagh ya nuna za suyi sha’awar wani na su ya rike Najeriya a zaben 2031
- Cif Olusegun Obasanjo ya karbi ‘yan kungiyar, ya fada masu yana goyon bayan a kai shugabanci Kudu
Ogun - Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya yi kira ga mutanen Najeriya da suyi hattara wajen zaben sabon shugaban kasa.
Cif Olusegun Obasanjo ya bada shawara cewa ka da mutane suyi amfani da son zuciyarsu wajen zaben ‘dan takara, The Cable ta fitar da rahoton a jiya.
Obasanjo ya yi wannan bayanin a lokacin da jagororin kungiyar Mzough U Tiv suka kai masa ziyara a dakin karatunsa da yake Abeokuta a jihar Ogun.
An rahoto tsohon shugaban kasar yana cewa yana mai goyon mulkin Najeriya ya tashi daga hannun mutanen Arewa, ya koma hannun ‘Yan Kudu.
A jawabin da Kehinde Akinyemi ya fitar, Obasanjo ya nuna bai dace al’umma su bari son kai ya cigaba da kashe kasa, kyau a zabi wanda ya cancanta.
Mulki ya cigaba da zama a Arewa?
Jam’iyyun PDP da NNPP sun tsaida Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso daga Arewacin Najeriya yayin da yankin ke rike da mulki tun 2015.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A gefe guda, jam’iyyar APC mai mulki ta tsaida Bola Tinubu a tikitin Musulmi da Musulmi, sai kuma Peter Obi daga yankin Kudu yana takara a inuwar LP.
Wata rana Tiv za suyi mulki
Obasanjo ya kuma fadawa ‘Yan Mzough U Tiv da su nemi mulki ya zo yankinsu na Arewa ta tsakiya.
Shugaban wannan tafiya, Iorbee Ihagh yace sun zo wajen Cif Obasanjo ne a matsayinsa na jagora, ganin irin yadda yake kaunar ‘Yan kabilarsu ta Tiv.
Iorbee Ihagh ya nuna za su so mulki ya rika zagayawa a Najeriya ta yadda zuwa 2031 za a ce daga bangaren Arewa maso tsakiya za a samu shugaban kasa.
Daily Post ta rahoto dattijon yana cewa abin da zai ceci dinbin al’ummar Najeriya nan gaba shi ne noma, yace za a daina maganar mai da gas, sai abinci.
Tsofaffin shugaban kasa na tare da Obi
An samu rahoto cewa Pat Utomi wanda jigo ne a tafiyar Peter Obi da LP, yace wasu da suka rike mulkin Najeriya suna goyon bayansu a zabe mai zuwa.
A cewar Farfesa Pat Utomi, Jam’iyyar adawa ta LP tayi tanadi ta yadda za Peter Obi da Datti Baba Ahmed za suyi nasara a kan jam'iyyun APC da su PDP.
Asali: Legit.ng