Jihar Kaduna Zata yi Kewar El-Rufai Bayan Cikar Wa’adin Mulkinsa, Sanata Uba Sani
- ‘Dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani, yace jihar Kaduna zata yi kewar Nasir El-Rufai bayan cikar wa’adin mulkinsa
- Sanatan mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa yace gwamnan yayi kokari a fannin ilimi, raya birane da sauransu
- Mai fatan zama gwamnan gobe na Kadunan yace a fannin batun tsaro ya zama tilas a kirkiri ‘yan sandan al’umma tare da basu makamai
Kaduna - ‘Dan takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani, yace za a yi matukar kewar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai idan ya sauka daga kujerarsa, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Gwamnatin El-Rufai zata cika wa’adin mulkinta a watan Mayun 2023, shekaru 8 bayan hawarsa karagar mulkin jihar Kaduna.
Sani ya kwatanta El-Rufai da mai gaskiya da rikon amana kuma mutumin da ya bautawa jihar yadda ya dace.
Kamar yadda yace, gwamnan yayi kokari mai yawa wurin kawo cigaba a jihar duk da ta yuwu ya tafka wasu kurakurai a matsayinsa na ‘dan Adam.
Sanata Uba Sani yayi wannan tsokacin ne a wani taron manema labarai wanda Kungiyar ‘yan jarida ta kasa ta shirya domin dukkan ‘yan takarar gwamna a jihar.
“Gwamna El-Rufai mutum ne mai gaskiya kuma ba za a iya zarginsa da rashawa ba. Yayi Ministan babban birnin tarayya kusan shekaru 15 da suka gabata amma har yanzu kewarsa ake yi. Za a yi kewarsa a jihar Kaduna idan wa’adin mulkinsa ya cika.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- Yace.
Ya kara da cewa, Gwamnan yayi abubuwa masu yawa wurin raya birane, ilimi, lafiya da sauran bangarori.
Sani ya magantu kan tsaro
A fannin tsaro, Sani yace samar da tsarin tsaro na jiha shi ne kadai zai samar da maganin ‘yan bindiga a arewacin Najeriya ballantana a jihar Kaduna.
Ya kara da kwatanta fannin shari’ar kasar nan matsayin nakasassa inda yace dole ne a gyara dokoki domin a saka ‘yan sa kai a fannin tsaro.
Ya yi bayanin cewa, a matsayinsa na Sanata dake wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, yayi abubuwa masu yawa wurin ganin cewa an tabbatar da dokar da zata bai wa ‘yan sa kai damar rike makamai.
Kamar yadda yace, don tabbatar da tsaro kan ta’addancin da ‘yan bindiga ke aiwatarwa a yankin karkara, ya zama dole a kirkiro ‘yan sandan yanki.
Ya kara da kira kan gujewa siyasantar da lamarin tsaro a kasar nan idan tana cikin mawuyacin halin shawo kan matsalar.
Kotu ta jaddada Uba Sani matsayin ‘dan takarar gwamnan Kaduna
A wani labari na daba, wata babbar kotun tarayya ta jaddada Uba Sani matsayin ‘dan takarar gwamnan jihar Kaduna a APC.
Kotun tayi fatali da karar Muhammad Sani Sha’ Aan wanda ya kalubalanci nasarar Uba Sani a zaben fidda gwani
Asali: Legit.ng