Bidiyon Gabatarwar Da Ƴar Takarar APC Ta Yi Wa Peter Obi A Coci Ya Janyo Cece-Kuce A Soshiyal Midiya

Bidiyon Gabatarwar Da Ƴar Takarar APC Ta Yi Wa Peter Obi A Coci Ya Janyo Cece-Kuce A Soshiyal Midiya

  • Yan Najeriya sun rika yin mahawara kan bidiyon gabatarwa da tsohuwar yar takarar majalisa a APC ta yi wa Obi a coci
  • Mafi yawancin magoya bayan dan takarar shugaban kasar na LP suna zargin Benjamins-Laniyi tana da wani mugun nufi a zuciyarta
  • Wasu kuma masu amfani da soshiyal midiya sun ce babu laifi kan gabatarwar domin Obi kamfen ya tafi yi a cocin ba ibada ba

A ranar Asabar 2 ga watan Disamba, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party ya halarci taron wakokin bushara 'The Experience' da cocin House on the Rock Church a Legas ta shirya.

A wurin taron, Adebayo Benjamins-Laniyi, tsohowar yar takarar majalisa a babban birnin tarayya Abuja, ta sanar da cewa Obi ya halarci taron.

Obi da Benjamins
Bidiyon Gabatarwar Da Ƴar Takarar APC Ta Yi Wa Peter Obi A Coci Ya Janyo Cece-Kuce A Soshiyal Midiya. Hoto: Dayo Benjamins-Laniyi, Peter Obi.
Asali: Facebook

Yayin da ta ke gabatar da dan takarar shugaban kasar na Labour Party, Benjamins-Laniyi ta ce gabatar da tsohon gwamnan na jihar Anambra da ta yi don siyasa ne ba don kashin kai ba.

Kalamanta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Don siyasa ne ba don kashin kai ba, yau, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Mr Peter Obi. Na gode."

Yan Najeriya sun yi martani

Yayin da Benjamins-Laniyi nan take ta bar minbarin bayan jawabin, yan Najeriya da dama, galibi magoya bayan Obi (Obidients), sun tafi soshiyal midiya suna tambayan ma'anar gabatarwar da ta yi wa Obi.

Wani mai amfani da Twitter, Stanley Chuck ya ce:

"Yayin da ta ke gabatar da mai gidan mu, wannan matar yar APC ta ce "siyasa ne, ba don kashin kai ba." "Misalin "ya shirya teburi ne a gaban makiya na."

Wani a Twitter mai suna @IruefiNG ya ce:

"Idan da niyya mai kyau gare ki, ba za ki yi gargadi ba "ba siyasa bane don kashin kai ne" kafin gabatar da kowa, maganan gaskiya, mun san akwai abin da kika kulla a zuciya, kiyayyan daga zuciya ne, rashin kaunar daga zuciya ne."

Akasin mutane da dama, @Sholexx_ ya yi imanin tsohuwar mai neman takarar na APC ta yi dai-dai wurin gabatar da Peter Obi.

Ya ce:

"Ba bayyana ainihin abin da ya kawo Mr Peter Obi wurin taron. Abin da ta ke nufi shine Mr Peter Obi ya taho wurin kamfen ne ba ibada ba.
"idan ka tambaye ni, zan ce gaskiya ta fada 100% #experience17."

Majiya Ta Bayyana Dalilin Da Yasa NCAA Ta Tsare Jirgin Kamfen Din Peter Obi

Bayanai sun fito dangane da dalilin da yasa hukumar NCAA ta tsare jirgin saman kamfen na dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi.

Mista Diran Onidade, jami'an watsa labarai na kamfen din Obi-Datti ya fitar da sanarwa inda ya koka kan tsare jirgin da ya ce ya janyo wasu jiga-jigan jam'iyyar sun gaza halartar kamfe a Ibadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel