Gwamnonin PDP 2 Sun Kalubalanci Buhari Kan Ya Fallasa Gwamnoni Masu Satar Kudin Kananan Hukumomi

Gwamnonin PDP 2 Sun Kalubalanci Buhari Kan Ya Fallasa Gwamnoni Masu Satar Kudin Kananan Hukumomi

  • Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas tare da takwaransa na jihar Binuwai, Samuel Ortom, sun ce Buhrai ya fito ya fallasa sunayen gwamnoni dake satar kudin kananan hukumomi
  • Gwamnonin biyu na tsagin G5 ta jam’iyyar PDP, sun alakanta abinda Buhari yayi da bacin suna ga gwamnonin tunda kudin goro yayi musu
  • Dukkansu su biyu sun ce tun daga hawansu mulki a 2015 basu taba tsakurar kudaden kananan hukumomi ba duk da yanzu kai tsaye ake tura kudaden daga gwamnatin tarayya

Ribas - Gwamnonin jihohin Ribas da Binuwai, Nyesom Wike da Samuel Ortom, sun kalubalanci Shugaba Buhari da ya fallasa gwamnonin da suke da alhakin sace kudaden kananan hukumomi, Channels TV ta rahoto.

Wike, Buhari da Ortom
Gwamnonin PDP 2 Sun Kalubalanci Buhari Kan Ya Fallasa Gwamnoni Masu Satar Kudin Kananan Hukumomi. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Gwamnonin dake cikin kungiyar gwamnonin PDP ta G5 sun kalubalancin Buharin ne a ranar Juma’a yayin kaddamar da titunan Mgbusosimini dake jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Daya Bayan Daya, Gwamnoni Suna Maidawa Buhari Martanin Zargin da Yayi Masu

A ranar Alhamis ne Shugaba Buhari yayin jawabi yace gwamnoni ne ke sace kudin da aka ware na kananan hukumomi.

Daily Trust ta rahoto cewa, amma yayin martani kan lamarin, Gwamna Wike ya musanta taba daukar kudin kananan hukumomi tun bayan hawansa mulkin jiharsa a 2015. Ya kalubalanci shugaban kasa da ya bayyana sunayen gwamnonin dake wannan dabi’ar saboda fadin hakan bacin sunan gwamnonin ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina son kalubalantar shugaban kasa, shugaban kasa kai ne shI Gaba a kuma mun yarda matsayinka na shugaba dole ka fito ka sanar da ‘yan Najeriya su waye suke aikata wannan laifin? Kace gwamnoni suna kwashe kudaden kananan hukumomi, ina son cewa koda na rana daya ban taba diban kudin kananan hukumomi ba kuma bani da dalilin yin hakan.
“Toh shugaban kasa su waye wadannan? Ka san su, ka fada mana. Babu kyau bata suna ga mutane masu yawa tunda kace gwamnoni, ni bana cikin wadannan gwamnonin. Shugaban kasa ka sanar cewa gwamnoni masu nagarta basu cIkin wadannan.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Ya Tona Asirin Gwamnonin Dake Sace Kudin Kananan Hukumomi

- Wike yace.

Ya kara da cewa, a matsayinsa na shugaban karamar hukuma karkashin Gwamna Peter Odili, Gwamna bai taba taba masa kudi ba kuma bashi da dalilin da zai da ya taba na wasu yayin da yake gwamna.

Ortom yayi bayani

A yayin goyon bayan jawabin takwaransa, Gwamna Ortom na jihar Binuwai ya musanta taba kudin kananan hukumomi inda yace kudadensu suna zuwa musu ne kai tsaye daga lalitar gwamnatin tarayya.

Ortom yace:

“A gaskiya ba gaskiya bane a ce dukkan gwamnonin masu laifi ne, dukkan gwamnoni suna satar kudin kananan hukumomi. Na zama Gwamna tun 2015, EFCC tazo, ICPC ta zo tare da duk wata hukuma da zasu iya bankado harkalla a Binuwai. Babu amfani yin kudin goro.
“Bana yi, ban so ba lokacin da gwamnatin tarayya tace kananan hukumomin su samu ‘yancinsu ba, amma daga rana ta farko kudadensu ana tura musu ne ba ta hannun kowa ba. Duk kudin da yazo daga asusun gwamnatin tarayya yana zuwa kai tsaye ne ga kowacce karamar hukuma.”

Kara karanta wannan

FG Tace Gwamnatocin Jihohi ne Suke kara Tsunduma ‘Yan Najeriya Cikin Matsanancin Talauci

Buhari yace gwamnoni ke kwashe kudin kananan hukumomi

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da cewa gwamnonin Najeriya ne ke lamushe kudaden kananan hukumomi.

Ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labaran gidan gwamnati a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng