Jam’iyyar APC Ta Sanar da Ranar da Za Ta Gudanar da Babban Gangamin Kamfen Dinta a Bayelsa
- Tawagar kamfen din APC ta Bola Tinubu za ta shilla jihar Bayelsa a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba domin gudanar da gangami
- Doifie Buokoribo, sakataren yada labaran AOC a jihar Bayelsa ne ya tabbatar da hakan a yau Laraba 30 ga watan Nuwamba
- A halin da ake ciki, gangamin Tinubu a Bayelsa dai ci gaba da kamfen ne na APC don cimma burinsa a zaben 2023 mai zuwa
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu zai shilla jihar Bayelsa domin gudanar babban gangamin kamfen dinsa a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da APC ke ci gaba da gangamin kamfen gabanin zaben 2023 mai zuwa nan da badi, rahoton PM News.
A cewar sanarwar da Doifie Buokoribo, sakataren yada labaran APC a jihar Bayelsa ya fitar a ranar Laraba game da zuwan Tinubu jihar, ya ce za su dura jihar ne don tallata hajar APC.
Ya kuma bayyana cewa, Tinubu zai zo da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima don ganawa da masu ruwa da tsaki da sarakunan gargajiya na jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan ganawa da jiga-jigan jihar, sanarwar ta ce:
"Daga can, za su wuce zuwa Oxhow Lake idan za a yi gangamin kamfen, inda Tinubu da sauran shugabannin jam'iyyar za su zanta da jama'ar Zamfara game da manufofin APC a 2023 kan kasar nan."
Sakon APC ga jama'ar Bayelsa
Buokoribo ya bayyana cewa, an kammala dukkan shirye-shirye don tarbar tawagar kamfen din da kuma yin gangamin cikin tsanaki.A cewarsa:
"Muna kira ga dukkan 'yan Bayelsa da mazauna yankin Ijaw da su fito kwansu da kwarkwata domin tarbar dan takarar shugaban kasan APC, Jagaban, cikin salama, a kan lokaci kamar yadda aka san kabilar Ijaw da karbar baki."
A tun farko tawagar kamfen ta APC a jihar ta ce tabbas APC za ta kawo kuri'un jihar a zaben 2023, rahoton Vanguard.
Ba zan yi muhawara da Peter Obi ba sai ya cika sharudda na 4, inji Bola Tinubu
Yayin da ake ci gaba da kamfen, akan zauna da 'yan takarar shugaban kasa don sanin makamarsu da kuma abin da suke son yi.
Tinubu ya ce ba zai wani tattaunawa da gidajen talabijin ba sai har ya samu wasu abubuwa da yake bukata.
Musamman Peter Obi, Tinubu ya bashi sharudda hudu a yake so ya kawo kafin su yi muhawara.
Asali: Legit.ng