Ba Zan Bar Bashin Ko Kwandala a Asusun Gwamnati Ba Ga Wanda Zai Gaje Ni, Wike

Ba Zan Bar Bashin Ko Kwandala a Asusun Gwamnati Ba Ga Wanda Zai Gaje Ni, Wike

  • Gwamna Wike na jihar Ribas yace ya shirya miƙa wa wanda zai gaje shi mulki ba tare da ciyo bashin ko sisi ba
  • Gwamnan, wanda ya nuna baga shakkar ko waye zai gaje shi yace, kuɗin da mutum ya tara ba shi ne ba, wane aiki ka yi
  • A ranar Talata, Wike ya faɗa wa mazzauna jihar Ribas su jira zai gaya musu wanda zasu zaɓa a matakin shugaban ƙasa

Rivers - Gwamnan jigar Ribas, Nyeson Wike, yace ya shirya yadda zai miƙa wa magajinsa mulki ba tare da ana bin jihar bashin ko naira ɗaya ba a 2023.

Channels tv ta ruwaito cewa Wike ya faɗi haka ne yayin kaddamar da Asibitin koyarwa na jam'iar jihar Ribas (RSUTH) da kuma rukunin gidajen ma'aikata.

Gwamna Wike na jihar Ribas.
Ba Zan Bar Bashin Ko Kwandala a Asusun Gwamnati Ba Ga Wanda Zai Gaje Ni, Wike Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

"Na faɗa wa mutane masu kishi cewa ba zan bar gidan gwamnati da bashi ba, bashin kwandala ɗaya ba zan bar wa magaji na ba. Ina son ya karbi mulki a tsaftace, inji Wike yayin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Abu Mai Sosa Zuciya: Hotunan Wani Matashi Bai Ci Abinci Ba Tsawon Kwana 2 ya Samu Taimako

"Ba zai zo yana ƙorafin ya tarad da tulin bashi har na biliyan N50bn ba, ba zan yi haka ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya bayyana cewa ya samu nasarori masu ɗumbin yawa a lungu da sako na jihar wanda ya kai matakin da masu sukarsa da kansu sun yaba masa.

"Nawa ka tara ba shi ne abin dubawa ba, manyan ayyukan raya ƙasa nawa ka aiwatar a ƙasa, su ne kaɗai bayan ka kauce zaka duba dama da hagu ka ji farin ciki da gamsuwa."
"Zaka ji baka kunyata mutanen da suka baka amana ba, na ɗauki alkawurra kuma na cika. Zan sa hannu a Aljihu na fito ina tafiya a Titi da kwarin guiwa kuma na gode wa Allah bisa damar da ya bani."

- Wike.

A ranar Talata da ta gabata, Gwamna Wike ya roki al'ummar jihar Ribas su zaɓi 'yan takarar PDP a zaɓukan gwamna, yan majalisun tarayya da na jihohi a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Bindige Wani Fitaccen Mawaki Har Lahira a Najeriya

A cewarsa ba ya shakkar ko waye zai zama magajinsa a babban zaben dake tafe, kamar yadda Sunnews ta ruwaito.

FG Ta Dorawa Gwamnatocin Jiha Laifin Wurga ‘Yan Najeriya a Talauci

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta zargi gwamnonin jihohi da kara tura mutane cikin matsanancin talauci

Ƙaramain ministan tsare-tsare da kasafi na ƙasa, Clemen Agba, yace sama kaso 70 cikin 100 da mutanen dake fama da talauci suna rayuwa ne a karkara.

Yace maimakon gwamnonin su maida hankali wajen tsamo mutane daga ƙaƙanikayi, sai suka maida hankali wajen gina abubuwan da suka shafi birane kaɗai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262