Ma’aijin Jam’iyyar NNPP Ta Su Kwankwaso Ya Saki Layi, Ya Bayyana Yin Murabus

Ma’aijin Jam’iyyar NNPP Ta Su Kwankwaso Ya Saki Layi, Ya Bayyana Yin Murabus

  • Jigon siyasa kuma ma'ajin jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar ta su Kwankwaso
  • Jam'iyyar APC ta nuna sha'awarta kan dawowar Ningi karkashin inuwarta domin ci gaba da zama cikakken mamba kamar yadda yake a baya
  • Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba fuskantar sauye-sauyen sheka gabanin babban zaben 2023, lamarin da ke kada hantar 'yan takara da dama

Ningi, jihar Bauchi - Ma'ajin jam'iyyar NNPP na kasa, Shehu Ningi, ya bayyana yin murabus daga mukaminsa tare da fita da fitarsa daga jam'iyyar.

Yin murabus din Ningi na iya shafar nasarar Rabiu Musa Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta NNPP.

A cikin takardar yin murabus dinsa tare barin jam'iyyar ga gundunar Ningi ta karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi, jigon na NNPP ya bayyana cewa, ya bar jam'iyyar ne saboda wasu dalilai na kashin kansa.

Jam'iyyar su Kwankwaso ta samu babban gibi yayin da ake tun karar zaben 2023
Ma’aijin Jam’iyyar NNPP Ta Su Kwankwaso Ya Saki Layi, Ya Bayyana Yin Murabus | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Burinmu Ningi ya dawo APC nan kusa, inji APC

A bangare guda, tawagar kamfen ra jam'iyyar APC ta yada hoton takardar a Twitter tare da bayyana fatan Ningi ya dawo cikinta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar APC, Ningi ya kasance jigo kuma mamban APC a baya, kuma a yanzu ma suna maraba da dawowarsa jam'iyyar don ci gaba da zama dan gida.

APC ta rubuta a Twitter cewa:

"Ma'ajin NNPP na kasa, Hon Shehu Barau Ningi ya fice daga jam'iyyar, muna fatan ya dawo gidansa na dawo inda a ko yaushe ake masa maraba"

Jam'iyyun siyasa a Najeriya na ci gaba da fuskantar sauya sheka yayin da ake ci gaba da tunkarar babban zaben 2023, shekarar da Manjo Buhari mai ritaya zai sauka a mulki gaba daya.

Ya zama wajibi Musulmi ya zabi Tinubu a zaben 2023, inji MURIC

A wani labarin na daban, kungiyar kare hakkin Musulmai ta yi duba ga 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2023, ta bayyana wanda ya kamata a zaba.

MURIC ta ce Musulmai, musamman Yarbawa ba su da zabin da ya wuce su zabi Tinubu a zaben 2023 mai zuwa badi.

MURIC ta bayyana hakan ne tare da fadin dalilanta bayan tunawa da yadda Musulmai a yankin Kudu maso Yamma ke fama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel