Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Karbi Jiga-Jigan PDP da Wasu Jam'iyyu a Kwara

Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Karbi Jiga-Jigan PDP da Wasu Jam'iyyu a Kwara

  • Manyan jiga-jigan jam'iyyun adawa da dama sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki ranar Alhamis a Kwara
  • Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq ya musu maraba tare da basu tabbacin ba za'a nuna musu banbanci ba
  • Daga cikin mutanen da suka sauya shekar harda tsoffin kwamishinoni, yan takara da shugabanni maza da mata

Kwara - Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kwara ta yi maraba da masu sauya sheka daga jam'iyyun siyasa daban-daban a Ilorin, babban birnin jihar ranar Alhamis.

Jaridar Tribune Online tace tsofafftin jiga-jigai a jam'iyyar PDP, NNPP, ADC da Sauran jam'iyyu ne suka jagoranci dandazon masu sauya sheƙar zuwa APC.

Sauya sheka a Kwara.
Sauya Sheka: Jam'iyyar APC Ta Karbi Jiga-Jigan PDP da Wasu Jam'iyyu a Kwara Hoto: tribune
Asali: UGC

A wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na gwamna, Rafiu Ajakaye, ya fitar yace masu sauya shekar sun ce dumbin nasarorin gwamnatin APC a ɓangaren lafiya, Ilimi, jin daɗin ma'aikata da sauransu ne suka ja hankalinsu.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Jerin Manyan Jiga-jigan APC 6 Da Basa Goyon Bayan Tinubu Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi

Sanarwan tace 'yan siyasan sun fito ne daga shiyyoyi uku na jihar Kwara kuma gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ne ya karɓe su a hukumance.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasu daga cikin jiga-jigan da suka koma APC

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa daga cikin masu sauya shekar akwai tsohon mataimakin kakakin majalisa, Mathew Okedare, tsoffin kwamishinoni da hadiman tsohon gwamna, Abdulfatah Ahmed.

Wasu shugabannin PDP, yan takarar majalisa na jam'iyyu kamar SDP, ADC, YPP da sauran mambobin maza da mata na daga cikin mutanen da suka shiga APC.

Da yake musu maraba a hukumance, Gwamna AbdulRazaq ya taya sabbin mambobin APC murna tare da alƙawarin ba za'a nuna musu banbanci ba.

"Muna muku maraba tare da yaba muku bisa yardar da kuka nuna wa jam'iyyarmu. Zamu yi aiki tare domin kai wa ga nasara, zamu ɗauke ku yan uwa."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin wasu jihohi 5 na APC da Tinubu zai iya rasa kuri'unsu badi

"Kamar yadda kuke gani jam'iyyar PDP ta zama kwanko, da kafafen sada zumunta kaɗai suke iya amfani wajen ikirarin shahara."

- Gwamn AbdulRazaq.

Atiku da Tinubu sun kara shiri a kwamitin kamfe

A wani labarin kuma Atiku Abubakar da Bola Tinubu Sun Yi Sabbin Naɗe-Naɗe a Tawagar Yakin Neman Zaben 2023

Manyan yan takara biyu da ake hasashen sune a sahun gaba wajen tseren gaje Buhari sunƙara naɗe-naɗe a yakin neman zaɓensu

Tinubu ya naɗa kakakin tawagar arewa ta yamma yayin da Atiku ya naɗa mai ba da shawara na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel